Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 14 na majalisar dokokin jahar Nassarawa

Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 14 na majalisar dokokin jahar Nassarawa

Jam’iyyar APC ta lashe kujeru goma sha hudu daga cikin kujeru ashrin na majalisar dokokin jahar Nassarawa da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu INEC ta sanar da kujeru 20 daga cikin kujeru 24 da majalisar ta kunsa, yayin da zabe bai kammalu a mazabu guda hudu na jahar ba, inda a yanzu INEC take nazari kan ranar da zata maimaita zaben.

KU KARANTA: INEC ta mika ma hadiman Buhari su 2 shaidar lashe zaben yan majalisar wakilai

Kujeru goma sha hudu da APC ta lashe sun hada da kujerar mazabar Umaisha/Ugya, Toto/Gadabuke, Nasarawa ta tsakiya, Udege/Loko, Keffi ta yamma, Kokona ta gabas, Akwanga ta Arewa, Lafia ta tsakiya, Lafia ta Arewa, Keana, Awe ta Arewa, Awe ta kudu, Wamba da Uke/Karshi.

Inda PDP ta kashe Akwanga ta kudu, Nasarawa Eggon ta yamma, Doma ta yamma, Obi 1 da Kokona ta yamma sai jam’iyyar ZLP da ta lashe zaben mazabar Doma ta Arewa.

Sakamakon zaben ya nuna yan majalisu guda biyar sun sake lashe zabe, ma’ana zasu zarce akan kujerunsu, wadannan da suka kai bantensu sun hada da kaakakin majalisa Alhaji Ibrahim Balarabe-Abdullahi (APC-Umaisha/Ugya), Mohammed Okpoku (APC-Udege/Loko), Daniel Ogazi (APC-Kokona East), Tanko Tanko (APC-Awe ta Arewa) da Mohammed Alkali (APC- Lafia ta Arewa).

Sai kuma zabe a mazabun Obi 2, Karu/Gitata, Nasarawa, Eggon ta gabas da Keffi ya gabas sune wadanda basu kammalu ba, zuwa yanzu dai ta tabba jam’iyyar APC ce ta mamaye majalisar dokokin jahar Nassarawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel