Jama’an Ganduje da na Abba gida gida sun gudanar da addu’o’in samun nasara a zaben Kano

Jama’an Ganduje da na Abba gida gida sun gudanar da addu’o’in samun nasara a zaben Kano

Yayin da ake kirgan kwanakin da suka rage ma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta gudanar da zaben maimaici a wasu rumfuna 210 cikin kananan hukumomi 22 na jahar Kano game da zaben gwamnan jahar, yan siyasa sun shiga neman sa’a a wajen Allah ubangijin talikai.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito magoya bayan gwamnan jahar Abdullahi Umar Ganduje, da na dan takarar jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf sun gudanar da addu’o’in neman samun nasara a wurare daban daban, yayin da na Abba suka je filin gidan Sarki, na Ganduje kuma a Masallacin Dala suka yi.

KU KARANTA: Koda tsiya tsiya sai mun ci zaben nan – shugaban APC ta Kano

Jama’an Ganduje da na Abba gida gida sun gudanar da addu’o’in samun nasara a zaben Kano
Yan Gandujiyya
Asali: Facebook

Idan za’a tuna hukumar INEC ta sanar da rashin kammaluwar zaben gwamnoni a jahohi shida da suka hada da Kano, Benuwe, Sakkwato, Adamawa, Bauchi da Filato, sakamakon lalatattun kuri’un da aka kada a zaben sun fi yawa fiye da bambancin dake tsakanin yan takarar dake kan gaba.

Don haka INEC ta sanya ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da zata kammala wannan zabe, kafin sannan a jahar Kano, dan takarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ne ke kan gaba, yayin da gwamnan jahar, Abdullahi Umar Ganduje ke bi masa.

Jama’an Ganduje da na Abba gida gida sun gudanar da addu’o’in samun nasara a zaben Kano
Kwankwasawa
Asali: Facebook

Abba gida gida nada kuri’u 1,014,474, yayin da Ganduje ya samu kuri’u 987,819 kamar yadda alkalumman sakamakon zaben da INEC ta sanar ya nuna, don haka bambancin dake tsakaninsu bai kai yawan adadin lalatattun kuri’un da aka samu a zaben ba.

A yanzu dai hukumar INEC ta sanya ranar 23 ga watan Maris don gudanar da zaben maimaici, inda da haka ne za’a fitar da sahihin wanda ya lashe zaben zama gwamnan jahar Kano tsakanin Ganduje da Abba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel