Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 55, sun kubutar da mutane 760 a Zamfara

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 55, sun kubutar da mutane 760 a Zamfara

Dakarun rundunar soji ta ‘ofireshon sharan daji’ sun kashe ‘yan bidiga 55 tare da kubutar da wasu mutane 760 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Rundunar ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin jami’in yada labarai, Manjo Abiade, ya fitar yau, Talata, a Gusau.

Ya ce, dakarun soji sun yi nasarar kwace makamai, alburusai da kuma shanu da ‘yan bindigar sace daga mazauna kauyuka daban-daban. Ya bayyana cewar sun samu nasarar yin hakan ne ta hanyar dates dukkan hanyoyin fita daga dajin da ‘yan bindigar ke buya.

Mun kama mutane 24 da mu ke zargin na taimaka wa ‘yan bindigar ta hanyoyi daban-daban musamman bangaren bayar da bayanai da suke amfani da su wajen garkuwa da mutane da satar shanu kuma tuni mun mika su hannun rundunar ‘yan sanda domin cigaba da bincike.

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 55, sun kubutar da mutane 760 a Zamfara
Rundunar Sojoji
Asali: Twitter

“Dakarun sojin sun sama sun taimaka wajen nasarar da mu ka samu ta hanyar yin luguden wuta a sanannun maboyar ‘yan ta’adda da ke dazukan Kagara, Gando, Fankama, Fete da Dumburum.

“Daga cikin kayan da mu ka kwace daga hannun ‘yan ta’addar akwai bindiga samfurin AK 47 guda hudu, bindigar baushe 12, wata babbar bindiga ta musamman, baburan hawa 47, mota kirar Golf guda daya, shanu 61 da sauran su,” a cewar sa.

DUBA WANNAN: Mata sun mamaye ofishin INEC Sokoto, sun bukaci a sanar da Tambuwal ya ci zabe

Sannan ya kara da cewa, “sakamakon aikin rundunar mu, a kalla mutane fiye da 1000 sun samu damar komawa garuruwan su daga sansanin ‘yan gudun hijira.”

Manjo Abiade ya bayyana cewar sojoji uku da dan kungiyar bijilanti guda sun rasa rayuwar su yayin arangama da ‘yan bindigar a dajin Kagara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel