2019: Jihar Borno ta fada hannun Farfesa Babagana Umara-Zulum

2019: Jihar Borno ta fada hannun Farfesa Babagana Umara-Zulum

Farfesa Babagana Umara-Zulum shi ne wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Borno da aka yi a karkashin jam’iyyar APC mai mulki. Babagana Umara-Zulum ya samu kuri’a sama da Miliyan guda a zaben na makon jiya.

Wani abin ban sha’awa game da gwamnan na jihar Borno mai jiran-gado shi ne, ya kai mataki na Farfesa a jami’a kafin ya shiga harkar siyasa. Kusan dai wannan ne karon farko da aka samu Farfesan da ya zama gwamna.

Babagana Umara-Zulum yayi karatun sa ne a kwalajin nan na Ramat ta Maiduguri, inda yayi Difloma a 1988, bayan nan ya zarce jami’a yayi karatun kanikancin ruwa tsakanin 1990 zuwa shekarar 1994 a matsayin Digirin sa na fari.

KU KARANTA: ‘Dan takara ya samu kuri’a 100, 000 a bulus a zaben 2019

2019: Jihar Borno ta fada hannun Farfesa Babagana Umara-Zulum
Babagana Umara-Zulum zai gaji Gwamna Kashim Shettima
Asali: Twitter

Daga nan kuma sabon gwamnan ya tafi Jami’ar nan ta Ibadan inda ya samu Digir-gir a harkar ilmin kasa da kanikancin ruwa. A 2009 ya zama Daktan boko bayan ya sake komawa jami’ar sa ta gida UNIMAID domin samun PhD.

Shekaru 19 da su ka wuce Umara Zulum ya fara aiki a matsayin Malamun jami’a inda har ya kai matsayin Shehi na Farfesa. Daga baya kuma ya zama shugaban makarantar kwalejin nan ta Ramat kafin ya shiga gwamnatin Borno.

Gwamna Kashim Shettima ya nada sa kwamsihinan da zai kula da sha’anin dawo da jihar Borno cikin hayyacin ta bayan rikicin Boko Haram. A bara kuma gwamnan ya zabe sa domin ya gaje sa inda yanzu yayi nasarar cin zabe a jam'iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel