Jahar Imo ta angwance da sabon gwamna daga jam’iyyar PDP

Jahar Imo ta angwance da sabon gwamna daga jam’iyyar PDP

Tsohon kaakakin majalisar wakilan Najeriya, Emeka Ihedioha na jam’yyar PDP ne ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jahar Imo daya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, kamar yadda baturen zabe, Farfesa Francis Otonta ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito Farfesa Otonta ya bayyana haka ne da sanyin safiyar Talata a cibiyar tattara alkalumman sakamakon zaben gwamnan jahar dake garin Owerri, babban birnin jahar Imo.

KU KARANTA: Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 13, PDP ta samu nasara a jahohi 9

Jahar Imo ta angwance da sabon gwamna daga jam’iyyar PDP
Emeka Ihedioha
Asali: UGC

Da yake sanar da sakamakon zaben, Otonta yace Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP ya lashe zabe a kananan hukumomi goma sha daya cikin ashirin da bakwai na jahar Imo, inda ya samu jimillan kuri’u 273,404.

Wanda yazo na biyu a wannan zabe kuwa shine surukin gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha, Uche Nwosu na jam’iyyar AA, wanda ya lashe kananan hukumomi goma, tare da samun kuri’u 190, 364, yayin da tsohon gwamnan jahar Ikedi Ohakim na jam’iyyar Accord ya tashi da kuri’u 6, 846 kacal!

Dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Hope Uzodinma kuwa shi yazo na hudu da kuri’u 96, 458, yayin da na ukunsu shine Ifeanyi Ararume daga jam’iyyar APGA, wanda ya ci kananan hukumomi guda hudu tare da samun kuri’u 114, 676.

A gaba daya zaben an kada kuri’u 739,474, inda daga ciki aka samu haramtattun kuri’u 25, 130, sai kuma sahihai guda 714, 344, kamar yadda baturen zaben Farfesa Francis Otonta ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng