Jihohi 6 da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriya

Jihohi 6 da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriya

Babbar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta kaddamar da cewa, zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar, ga watan Maris bai kammala ba a jihohin Filato, Bauchi, Sakkwato, Adamawa da kuma Kano.

Hukumar INEC ta ce zaben bai kammala ba cikin jerin jihohi shida da ke Arewacin Najeriya a sakamakon aukuwar hargitsi da maimacin kada kuri'u da suka sanya aka soke zaben wasu rumfunan zabe.

Bisa ga tanadin doka da kuma shimfidar tsare-tsaren zabe, hukumar INEC ta ce zaben bai kammala ba cikin jerin jihohin sakamakon adadin kuri'u da aka soke ya haura tazarar da ke tsakanin manyan 'yan takara biyu masu rinjayen nasara.

Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Twitter

Biyo bayan soke kuri'u 49,377 inda tazarar adadin kuri'u da ke tsakanin 'yan takara masu rinjayen nasara ta kasance 44,929, Baturen Zabe na jihar Filato, Farfesa Richard Anande ya ce jam'iyyar APC ke kan gaba da kuri'u 583,225, yayin da jam'iyyar PDP ke da kuri'u 538,326.

Yayin da za sake zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, jam'iyyar PDP ke kan gaba da adadin kuri'u 469,512, inda jam'iyyar APC ke da kuri'u 465,453 kamar yadda Baturen Zabe na jihar Bauchi, Farfesa Muhammad Kyari ya bayyana.

Baturiyar zabe ta jihar Sakkwato, Farfesa Fatima Batul Mukhtar, ta ce za a sake zabe biyo bayan soke adadin kuri'u 75,403 inda jam'iyyar PDP ke kan gaba da kuri'u 489,558 yayin jam'iyyar APC ke da kuri'u 486,558.

A jihar Adamawa, za a sake zaben wasu rumfunan zabe 44 biyo bayan matsaloli da aka fuskanta yayin zabe na ranar Asabar. Shafin jaridar RFI Hausa ya ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ke gaba da kuri'u 367,471 yayin da APC ke da kuri'u 334,995 sai kuma jam'iyyar ADC mai kuri'u 113,205.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Babban Baturen zabe na jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu ya bayyana cewa, zaben jihar bai kammala ba sakamakon yadda adadin kuri'u da aka soke a wasu mazabu ya haura tazarar da ke tsakanin gwamna Ganduje da abokin adawar sa na jam'iyyar APC.

Farfesa Shehu ya ce adadin kuri'u 128,572 da aka soke ya haura tazara ta adadin kuri'u 33,006 da ke tsakanin manyan 'yan takarar masu hankoron samun nasara. Ya ce adadin kuri'u da aka soke kan iya sauya alkaluman zabe wajen tabbatar da rinjayen nasara a tsakanin 'yan takara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel