Siyasar Kano: Abin da ya faru jiya ya bamu kunya – Abdulmumin Jibrin

Siyasar Kano: Abin da ya faru jiya ya bamu kunya – Abdulmumin Jibrin

Yanzu haka dai hankalin jama’a ya karkata zuwa ga jihar Kano inda ake so a ji labarin wa ya lashe zaben gwamna tsakanin Gwamna mai-ci Abdullahi Umar Ganduje da Injniya Abba Kabiru Yusuf na PDP.

Ana haka ne dai jiya jami’an tsaro su ka kama mataimakin gwamnan jihar watau Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da kuma kwamishinan harkar kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, su na neman hanyar murde zaben da aka yi.

Wannan abu da ya faru ya jawo mutane su na ta tofa albarkacin bakin su inda ‘dan majalisar tarayya na jihar Kano mai wakiltar Kiru da Bebeji watau Honarabul Abdulmumuni Jibrin ya bayyana cewa abin da ya faru ya ba sa kunya.

An dai ga ‘yan sanda sun cafke mataimakin gwamna Ganduje da kuma Kwamishina Murtala Sule Garo, wanda ko riga babu a jikin sa. Hon. Abdulmumuni Jibrin yace dole kowa yayi tir da wannan abin Masha-Ah da ya faru jiya.

KU KARANTA: Sakamakon zaben Gwamnan Kano ya nuna PDP tayi gaba

Siyasar Kano: Abin da ya faru jiya ya bamu kunya – Abdulmumin Jibrin
Abdulmumuni Jibrin ya nemi a mikawa duk wanda ya ci zabe mulki a Kano
Asali: Depositphotos

Abdulmumuni Jibrin, wanda ya lashe zaben majalisar wakilai na tarayya da aka yi kusan makonni 2 da su ka wuce ya jawo hankalin gwamnati da shugabannin jihar Kano cewa dole su mikawa wanda ya ci zabe na 2019 mulki a Jihar.

Jibrin yayi wannan magana mai kama da jan-kunne ne a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwira. ‘Dan majalisar jihar yake cewa dole a kowane zabe akwai wanda zai yi nasara, sannan kuma za a samu wanda za a tika da kasa.

Haka zalika wani Hadimin shugaban kasa wanda ya fito daga jihar ta Kano, Bashir Ahmaad, ya bayyana cewa APC tayi abin kunya, inda yayi addu’a ga Allah da ya zabawa jama’a mafi alheri.

Maganar gaskiya an yi abin kunya... Tir! Allah ya kyauta, Allah kuma ya zaba mana mafi alheri. Allah ya tashe mu lafiya. Inji Bashir Ahmaad

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel