Karen batta: Kalli jerin manyan lauyoyi 18 da zasu kare Buhari a shari’arsa da Atiku

Karen batta: Kalli jerin manyan lauyoyi 18 da zasu kare Buhari a shari’arsa da Atiku

Turnuku fadin ibilisai, yaro bai gani ba balle ya raba, wannan shine kwatankwacin arangamar da za’a kwasa a gaban kotu tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris ne aka fara zaman sauraron karar da Atiku ya shigar gaban kotun sauraron koken zaben shugaban kasa, inda yayi zargin INEC da APC sun shirya magudin da ya baiwa Buhari nasara a zaben shugaban kasa.

KU KARANTA: Buhari ya gina katafaren Masallaci mai cin mutane 1000 a kauyen iyayensa

Karen batta: Kalle jerin manyan lauyoyi 18 da zasu kare Buhari a shari’arsa da Atiku
Buhari, Wole da Keyamo
Asali: UGC

Sai dai wasu majiyoyi masu tushe sun ruwaito tuni shugaban kasa Buhari ya kammala tara wasu tawagar gogaggun lauyoyi da farfesoshin sharia da wasu masu take musu baya da adadinsu ya kai goma sha takwas da zasu tsaya tsayin daka don kare martabar nasarar da Buhari ya samu akan Atiku.

Jagoran tawagar lauyoyin nan shine Cif Wole Olanipekun, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa mai lambar kwarewa ta SAN, sai kanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Akinola Osinbajo SAN, da kaakakin yakin neman zaben Buhari Festus Keyamo SAN.

Sauran sun hada da tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, Abubakar Mahmoud SAN, Femi Atoyebi SAN, Mike Igbokwe SAN, Niyi Akintola SAN, Yusuf Ali SAN, Osaro Egbobamien SAN, Dakta Muiz Banire SAN, Alex Iziyon SAN, Banbella Anachebe SAN, Charles Edosomwan SAN, Funke Adekoya SAN.

Har ila yau akwai Farfesa Taiwo Osipitan, Ibrahim Bawa SAN, da kuma Yakubu Maikyau, duba da jigogin shari’a dake cikin wannan tawaga, yasa ake ganin ba’a taba tara kwarrru, gogaggu kuma masana sharia a shari’ar shugaban kasa ba kamar wannan.

Shi jagoran ayarin lauyoyin, Wole Olanipekun sananne ne a harkar sharia, inda shien lauyan Buhari a karar da aka shigar dashi gaban kotu game da takardar shaidar kammala makarantar sakandari, kuma ya taba kare Tinubu a shekarar 2011 da aka shigar dashi kara gaban kotun da’ar ma’aikata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel