Malamin musulunci ya fadawa Buhari ya bi a hankali da bara-gurbi

Malamin musulunci ya fadawa Buhari ya bi a hankali da bara-gurbi

Mun ji labari cewa wani babban Malamin addinin musulunci a Garin Zariya, Mustapha Qasim ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara bayan ya lashe zaben da aka yi makonni 2 da su ka wuce.

Malamin musulunci ya fadawa Buhari ya bi a hankali da bara-gurbi
Sheikh Mustapha Qasim ya na so Shugaba Buhari ya duba sha'anin tsaro
Asali: Facebook

Dr. Mustapha Isa Qasim a hudubar juma’ar da yayi a masallacin ITN da ke cikin Zangon-Shanu da ke cikin Zariya a jihar Kaduna, ya nemi shugaba Buhari ya sa-ido domin ya tsince bata-garin da ke tare da shi da za a taba rasawa ba.

A hudubar wancan makon, wannan Malami ya kuma nemi shugaban kasar ya rika karbar shawarar mutanen kirki da za su taimaka masa wajen tafiyar da kasar. Dr. Qasim ya nunawa shugaban cewa akwai bara-gurbi a tare da shi.

KU KARANTA: Hajiya Aisha Buhari ta ari bakin mijinta tayi wata magana

Kamar yadda mu ka ji, Malamin addinin ya yaba da kokarin gwamnatin na shugaba Buhari, sanan ya kuma nemi a duba lamarin tsaro musamman a yankin su Zamfara da bangaren jihar Kaduna, inda ake kashe mutane dare da rana.

Shehin Malamin ya nuna godiyan sa ga Allah ga nasarar da shugaba Buhari ya samu, ya kuma yi kira ga jama’a su zabi wadanda su ka cancanta a zabukan gwamnonin jihohi da kuma ‘yan majalisun dokoki da za ayi a karshen makon nan.

Babban Malamin yayi wannan huduba ne a lokacin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu manyan ‘yan siyasar jihar irin su Sulaiman Abdu Kwari su kayi sallar juma’a a katafaren masallacin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel