'Yan ta'adda sun kai wa Abba Gida-Gida hari a jihar Kano

'Yan ta'adda sun kai wa Abba Gida-Gida hari a jihar Kano

A jiya Asabar, dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar adawa ta PDP, Abba Kabir Yusuf, ya tsallake rijiya da baya biyo bayan wani mummunan farmaki na masu ta'ada a tsaka da zaben gwamnoni da na yan majalisun dokoki na jiha.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Haruna Abdullahi, shine ya jibinci shaidar da wannan mummunan lamari yayin ganawar sa da manema labarai na kafar watsa labarai ta Channels TV a jiya Asabar cikin babban birni na Kanon Dabo.

Abba K Yusuf tare da Ubangidan sa; Sanata Rabi'u Kwankwaso
Abba K Yusuf tare da Ubangidan sa; Sanata Rabi'u Kwankwaso
Asali: Twitter

Jami'in na 'yan sanda ya bayyana cewa, kiris ya rage dan takarar da ya fi shahara da sunan Abba Gida-Gida ya afka tarkon miyagu inda jami'an tsaro suka yi gaggawar kai masa dauki yayin da yake yunkurin kada kuri'a a mazabar sa ta Unguwar Chiranchi da ke karkashin karamar hukumar Gwale.

Kazalika hukumar 'yan sandan jihar ta gargadi al'umma da su kauracewa duk wata bilinbituwa ta bayyana murna da farin cikin a kwararo da kuma lunguna gabanin bayyanar sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar a jiya Asabar, 9 ga watan Maris, 2019.

Hukumar 'yan sandan ta ce riko da wannan gargadi zai taimaka kwarai da aniyya wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankalin al'umma tare da nesantar da duk wata tarzoma ko tashin-tashin a birnin Kano da kewaye.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da ake kirdadon bayyanar sakamakon zaben gwamnan jihar daga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, tuni magaoya bayan jam'iyyar PDP sun fara busa sarewa da bugun kalangu na nasara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel