Gwamna Bagudu ya yi rashin shakikinsa

Gwamna Bagudu ya yi rashin shakikinsa

Allah ya yiwa kanin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Alhaji Faruku Bagudu rasuwa.

Daily Sun ta ruwaito cewa marigayin babban dan kasuwar ya rasu ne a daren jiya Laraba bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma tuni anyi jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ya koyar.

A yayin da ya ke mika sakon ta'aziyarsa ga gwamna Bagudu da iyalansa, Sanata Yahaya Abdullahi mai wakiltan Kebbi ta Arewa ya ce mutuwwar Alhaji Faruk babban rashi ne a ga jihar da kasa kamar yadda hadiminsa Jamil Yusuf Gulma ya sanar.

"Sanata Dr Yahaya Abdullahi da daukakin al'ummar Kebbi ta Arewa suna mika sakon ta'aziyarsu ga mai girma gwamnan Kebbi, Sanata Atiku Bagudu bisa rasuwar kaninsa, Alhaji Faruk Bagudu.

"Rasuwar Faruk Bagudu, wanda babban dan kasuwa ne a jihar Kebbi babban rashi ne ga kasa baki daya."

Sanatan ya yi addu'a Allah ya gafartawa marigayin ya kuma bawa iyalansa juriyar rashin sa.

Gwamna Bagudu ya yi rashin shakikinsa
Marigayi Alhaji Faruk Bagudu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Al'ajabi: 'Yan Najeriya 5 da ke ikirarin sun mutu, sun shiga aljannan sun dawo

Gwamna Bagudu ya yi rashin shakikinsa
Gwamna Bagudu tare da sauran al'umma a makabarta yayin da suke addu'a ga marigayi Alhaji Faruk Bagudu
Asali: Twitter

Gwamna Bagudu ya yi rashin shakikinsa
Al'umma da dama sun hallarci jana'izar marigayi Alhaji Faruk Bagudu kanin gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel