Waka a bakin mai ita: Yadda na kashe mai horas da kungiyarmu– Inji Dan kwallo

Waka a bakin mai ita: Yadda na kashe mai horas da kungiyarmu– Inji Dan kwallo

Wani matashi dan shekara 18, mai suna Salisu Muhammad ya fada komar Yansanda bayan an kamashi da laifin kisan mai horas da kungiyar da yake taka leda a cikinta a unguwar Yakasai ta jahar Kano, Mujittafah Musa.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Maris da misalin karfe 11:21 na dare yayin da musun kwallo ta hadasu, inda daga nan Salisu ya dauki wuka ya daba ma Mujittafa wuka a kirjinsa.

KU KARANTA: Mutum 1 ya mutu yayin da matasan APC dana PDP suka yi arangama a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris yayin da yake ganawa da manema labaru inda yace Mijitaba ya rasu ne akan hanyar kaishi Asibiti Murtala.

Sai dai Haruna yace an samu daman kama Salisu bayan ya sari wani matashi Suleiman Muhammed, sa’annan an kwace wukar da yayi amfani da ita. Sai dai wanda ake tuhuman ya bayyana cewa tun kimanin watanni 6 da suka gabata suka fara yar tsama da Mujitaba.

“Na tafka kurene a wani babban wasa da muka buga, wasan da mai horas da kungiyarmu Mujitaba ya dauketa da muhimmanci, amma sakamakon kuskuren da na tafka yasa aka ci mu, tun daga nan ya fara jin haushi na, yayi ta zagina, ni kuma na jefa masa rigan kwallona na fita.

“Daga nan sai na koma kungiyar kwallon dake muke hamayya da ita, kuma ina nuna masa adawa a duk lokacin da suke buga wasa, ko a asabar da ta gabata sai na yi musu adawa, har yayi alkawarin bani kashi idan ya kamani.

“Sai a daren muka hadu bayan an tashin wasan Real Madrid da Barcelona, inda yayi ta marina tare da dukana, ni kuma nan take na zaro wuka na caka masa a kirji" Inji shi.

A wani labarin kuma Rundunar Yansandan jahar Kano ta kama wasu miyagun matasa guda biyu marasa Imani da take zargi da kashe wani mutumi mai suna Adamu Bala yayin da yake gudanar da Sallar La’asar.

Sunayen wadannan miyagu shine Kamalu Musa da Babangida, dukkaninsu mazauna unguwar Shekar Madaki dake cikin garin Kano, inda suka ce sun kashe Adamu ne saboda ya ji ma wani abokinsu rauni a kwanakin baya a sanadiyyar dukansa da yayi babu gaira babu dalili.

Kaakakin Yansanda yace lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Feburairu, inda Babangida da Kamalu Musa suka lallaba suka kashe Adamu Bala a lokacin da yake salla a wani gidan buga bulo da yake aiki dake Bubugaje.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel