Ba wata hadaka da mu ka yi da APC – AAC ta gwasale Amaechi
Shugabancin jam’iyyar AAC (African Action Congress) ya yi Karin haske a kan matakin da jam’iyyar da APC ta dauka na cewar za ta mara wad an takarar ta na gwamna a jihar Ribas baya.
Jam’iyyar ta AAC ta ce ba ta shiga hadaka da APC ko wata jam’iyya ba a zaben gwamnonin da za a yi ranar Asabar mai zuwa.
A yayin wani taro da magoya bayan APC a jihar Ribas, jagoran jam’iyyar a jihar Ribas da ma yankin kudu maso kudu kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewar za su goyi bayan dan takarar jam’iyyar AAC, Awara Biokpomabo, a yayin da su ke jiran hukuncin kotu a kan dan takarar jam’iyyar su.
“A saboda haka a ranar Asabar, 9 ga wata, za mu zabi dan takarar jam’iyyar AAC. Ku koma azabunku ku zabi jam’iyyar AAC. Babu wani dalili da zai sa ku ki fita domin kada kuri’a, akwai tsaro. Ku yi shiri ku fita domin mu samu nasarar lashe zabe,” a cewae Amaechi.
Sai dai, a wani jawabi mai dauke da sa hannun, Dakta Malcom Fabiyi, mataimakin shugaba na kasa, da jam’iyyar AAC ta fitar ta ce: “Mun fahimci cewar jam’iyyar APC ta bukaci magoya bayanta a jihar Ribas su mara wad an takarar mu baya a zaben ranar Asabar, kamar yadda jagoranta a jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya fada.
DUBA WANNAN: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai da aka zaba a APC, ta bawa PDP
“Ba mu da ikon hana wata jam’iyya goyon bayan dan takarar da su ka ga dama, amma mu na son sanar da duniya cewar ba mu shiga hadaka da jam’iyyar APC ko wata jam’iyya ba a jihar Ribas,” a cewar Fabiyi.
Fabiyi ya kara da cewa, “abin da jam’iyyar AAC karkashin jagorancin Omoyele Sowore shine kafa sabuwar gwamnati mai tsari a matakin kasa da kuma jihohin Najeriya.”
“A saboda haka mu na kira ga dukkan ‘yan Najeriya ma su katin zabe da su fito a ranar 9 ga wata domin zabar ‘yan takarar jam’iyyar AAC domin samun shugabanci mai ma’ana.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng