Dahiru Bauchi: Shugaban kungiyar Izala ya fasa kwai a kan wasikar kulla yarjejeniya da El-Rufa'i

Dahiru Bauchi: Shugaban kungiyar Izala ya fasa kwai a kan wasikar kulla yarjejeniya da El-Rufa'i

Shugaban kungiyar jama’atu izalatul bid’a wa ika matus sunna (JIBWIS) reshen jihar Kaduna, Imam Tukur Isa, ya nesanta kungiyar su daga wata takardar kulla yarjejeniyar hana shugaban darikar Tijjaniya, Dahiru Bauchi, gudanar da taron mauludi a Kaduna.

Imam Tukur ya zargi mabiya shi’a da jam’iyyar PDP da shirya takardar da ke nuna cewar kungiyar Izala ta kulla yarjejeniya da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, a kan cewar za su goya ma sa baya a takarar da ya ke yi amma bisa sharadin cewar zai hana taron mauludin da Dahiru Bauchi ke yi a Kaduna.

Shugaban ya kara da cewa sun yi hakan ne domin haifar da rudani da gaba a tsakanin kungiyar Izala da mabiya darikar Tijjaniya domin cimma wata mummunar manufar su.

Dahiru Bauchi: Shugaban kungiyar Izala ya fasa kwai a kan wasikar kulla yarjejeniya da El-Rufa'i
Imam Tukur
Asali: Facebook

Shugaban ya yi wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi ga manema labarai bayan kamala wani taro da kungiyar Musulman Kaduna da aka yi a garin Kaduna. Kungiyoyin sun kira manema labarai domin nesanta kan su daga takardar da su ka ce PDP da shi’a ne su ka kirkire ta.

DUBA WANNAN: Sarakunan gargajiya sun ziyarci Buhari domin taya shi murna, hotuna

Malamin ya cigaba da cewar, wadanda suka fitar da wannan takarda sun yi ne bayan sun gano hadin kai ya kullu a tsakanin kungiyar Izala da mabiya darikar Tijjaniya a jihar Kaduna, musamman a bangaren goyon bayan gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa'i.

Imam Tukur ya kara da cewa PDP da shi’a ba su ji dadin kafa kungiyar hadin kai tsakanin Izala da ragowar dariku ba, kuma hakan ne ya sa su daukan nauyin yada karya da farfaganda domin ganin sun hada su rigima da juna da haddasa rudani a tsakanin Musulmin jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel