Da dumi dumi: Hukumar jarabawar WAEC ta saki sakamakon dalibai

Da dumi dumi: Hukumar jarabawar WAEC ta saki sakamakon dalibai

Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandari ta kasashen Afirka ta yamma, WAEC, ta sanar da sakin sakamakon jarabawar da hukumar ta shirya a tsakanin watan Janairu da Feburairu na shekarar 2019.

Sai dai duk da yadda ake yawan samun faduwa warwas a irin wannan jarabawar, wanda a baya a watanni Nuwamba da Disamba ake yi, amma a bana sakamakon jarabawar ta sauya zani.

KU KARANTA: Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban WAEC a Najeriya, Olu Adenipekun ne ya bayyana haka a ranar Talata, 5 ga watan Maris, inda yace cikin dubun dubatan daliban da suka zana jarabawar, an samu dalibai 39,557 da suka samu makin C a darussa biyar, hadi da Turanci da Lissafi.

Amma hukumar WAEC za ta gudanar da babban jarabawar da kusan duk wani dalibin da zai kammala sakandari a kasashen yammacin Afirka zai zana ne a cikin watan Afrilun shekarar 2019, inda zai dauka har cikin watan Yuni.

Ga duk wanda ya samu makin C a darussa biyar karanci, hadi da samun kyakkyawan maki a jarabawar shiga makarantar gaba da sakandari ta JAMB, ana sa ran zai iya samun gurbin cigaba da karatu a jami’a, kwalejin kimiyya, kwalejin fasaha ko kuma kwalejin ilimi, ko ma ya makarantun kasashen waje.

Baya ga jarabawar WAEC, akwai kuma jarabawar NECO, wanda hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandari ta Najeriya ke shiryawa, amfanin NECO shine kana iya hada shi da WAEC ka tashi sakamakon jarabawa mai kyau.

Ko kuma idan sakamakon jarabawar WAEC tayi ba zata, toh NECO tana iya maye gurbinta, don haka ake kira ga dalibai maza da mata dasu dage kwarai wajen zana dukannin jarabawannan guda biyu, domin suna da amfani matuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel