Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa (Hotuna)

Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin wasu manyan baki daga majalisar sarakunan gargajiyan Najeriya a karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, a fadar gwamnati dake Abuja.

Legit.ng ta ruwaito Sarakunan sun kai masa ziyarar ce irin ta jinjina da ban girma tare da tayashi murnar sake lashe zaben shugaban kasa karo na biyu, wanda hakan ya bashi daman cigaba da mike kafa a madafan iko har shekarar 2023.

Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa (Hotuna)
Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abubuwa 7 da zasu tabbatar da wanda zai lashe takarar gwamnan jahar Kaduna

Ita dai majalisar sarakunan Najeriya an kafata ne da nufin karfafa zaman lafiya, da kwanciyar hankali tsakanin yan Najeriya, bada shawara akan harkokin da suka shafi gargajiya, tarbiyyantar da jama’a, da kuma yin sulhu a tsakanin jama’a.

Sultan na shugabantar majalisar ne tare da Oni na Ife, Adeyeye Enitan Ogunwui, sakataren majalisar shine Oba Aderemi Adedapo, Alademore na do-Osun, kamar yadda tsarin shugabancin majalisar yake.

Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa (Hotuna)
Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa
Asali: Facebook

Sauran yan majalisar zartarwa na majalisar sun hada da Sarkin Kano, Mohammad Sanusi II, Shehun Bornu, Alhaji Abubakar IBN, Umar Gabar, El-Kanemi, Oba na Benin, Omo N’Oba N’edo Uku Okpolokpolo Erediauwa, Obong na Calabar, Edidem Ekpo Abasi OUT V, Etsu na Nupe, Alhaji (Dr) Yahaya Abubakar, Obi na Onitsha, Igwe Nnaemeka Achebe, Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussein Adamu.

Wasu daga cikin sarakan da suka halarci zaman akwai na Zaria, Alhaji Dakta Shehu Idris, Gbon gom Jos, sai kuma Sheikh Isah Ali Pantami da sauran manyan Sarakuna daga yankin kudancin kasar nan.

Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa (Hotuna)
Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa
Asali: Facebook

A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Jama’til Nasaril Islam, Alhaji Sa’adu Abubakar III ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara a zaben 2019 daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu.

Sai dai Sarkin Musulmai yayi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya sha kayi a hannun Buhari, daya rungumi kaddara, ya saduda, kuma ya rungumi zaman lafiya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kungiyar JNI ta fitar a ranar Lahadi a babban ofishinta dake garin Kaduna ta bakin babban sakataren hukumar, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, inda yace JNI na godiya ga Allah daya tabbatar da zaman lafiya a zaben daya gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel