IBB ya taya Buhari murnar lashe zabe

IBB ya taya Buhari murnar lashe zabe

- Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya shiga sahun masu taya Shugaba Buhari murnar zarcewa kan karagar mulki

- Babangida ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari ya yi sulhu da dukkan abokan hammayarsa ya kuma jawo su jiki domin ci da kasa gaba

- Tsohon shugaban mulkin sojan ya kuma shawarci Buhari ya duba batun sauya tsarin rabon arzikin kasa da wasu batutuwan da ke adabar kasar

Tsohon shugaban kasa na mulkin soji na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya mika sakon taya murna da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan nasarar da ya samu na sake lashe zabe karo na biyu.

A cikin wani sakon mai tsawo da ya tabo wasu dalilan da ya janyo rashin jituwa tsakanin shugabanin kasar a bara, Babangida ya bukaci Buhari ya yi kokarin sulhunta kasar sannan ya sauya tsarin rabon arzakin kasa tare da kirkiran sabbin hanyoyi na inganta tattalin arzikin kasar.

IBB ya taya Buhari murnar lashe zabe
IBB ya taya Buhari murnar lashe zabe
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari

Tsohon shugaban mulkin sojin ya ce wadanda ke neman a sauya tsarin rabon arzikin kasa suna da hujjar neman ayi a hakan har ma ya siffanta su da 'yan Najeriya masu hankali.

Babangida kuma ya bukaci Buhari ya dai-dai ta tsakanin al'umma musamman game da rikice-rikicen da za su biyo bayan sakamakon zabe.

"Ya kamata sabon shugaban kasar ya rungumi dukkan abokan hammayarsa duk da irin musayar kalamai da su kayi a yayin yakin neman zabe.

"Dole shugaban kasa ya guji daukansu a matsayin makiyarsa ko ma 'yan adawa sai dai ya yi aiki tare da su a matsayin masu kishin kasa da suke da mabanbantan ra'ayi a kan yadda za a ciyar da kasar gaba."

Ya kuma yabawa babban dan takarar hammaya, Atiku Abubakar inda ya karama shi da kalmomi kamar 'jarumi, mai juriya, mara fargaba' ya kuma kara da cewa yana da magoya baya daga dukkan kabilu da addinai na Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel