Wani miji ya kashe matarsa saboda hana shi raya sunar aure

Wani miji ya kashe matarsa saboda hana shi raya sunar aure

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Neja ta ce ta kama wani magidanci mai shekaru 35 a duniya, Mohammed Manu da aka ce ya kashe matarsa, Bulo a kauyen Barusa da ke karamar hukumar New Bussa da ke jihar.

'Yan sandan sun tabbatar da kama shi ne a ranar Alhamis inda aka ce tawagan 'yan sanda da ke ofishin 'yan sanda na New Bussa ne suka damko wanda ake zargin.

Ana zargin Manu ya halaka matarsa ne saboda ta hana shi saduwa da a lokuta da dama da ya yi yunkurin hakan.

Wani miji ya kashe matarsa saboda hana shi raya sunar aure
Wani miji ya kashe matarsa saboda hana shi raya sunar aure
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Taron sulhu: Atiku ya gabatarwa Buhari wasu muhimman bukatu 5

An gano cewar hana Bulo samun damar raya sunnar aure tare da ita ne ya yi sanadiyar mutuwar ta.

Wanda ake zargin ya shaidawa Punch cewar ya harbe matarsa da bindigan hannu bayan ta bata masa rai saboda hana shi saduwa da ita.

Manu ya ce, "Nayi mata gargadi ta dena hana ni saduwa da ita tunda hakan yana cikin manyan haki na aure. Duk lokacin da na nemi in kusance ta sai ta rika wulakanta ni, ni kuma ba zan amince da hakan ba.

"Da na matsa sosai a ranan, sai ta ture ni hakan kuma ya sa rai na ya yi matukar baci sai na kashe ta. Dama ta saba kirkiran dalilai duk lokacin da ne nemi in kusance ta.

"Mene zai sanya mata na ta hana ni in kusance ta? Wannan abin kunya ne a garin mu; ba ta da ikon yi min hakan."

'Yan sanda sun ce an gurfanar da Manu a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel