Taron sulhu: Atiku ya gabatarwa Buhari wasu muhimman bukatu 5

Taron sulhu: Atiku ya gabatarwa Buhari wasu muhimman bukatu 5

- Atiku Abubakar ya gabbatar da wasu bukatu 5 da ya ke nema daga Shugaba Muhammadu Buhari a yayin taronsa da Abdulsalami Abubakar da kwamitinsa na zaman lafiya (NPC)

- Bukatun da ya nema sun hada da bude asusun ajiyar kudi na 'yan jam'iyyar hamayya, janye sojoji daga wurin zabukka da za a yi nan gaba da sauransu

- Ana sa ran kwamitin zaman lafiyar ta NPC za ta gana da Shugaba Muhammadu Buhari domin gabatar masa da bukatun na Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da ya sha kaye a zaben 2019, Atiku Abubakar ya gabbatar da wasu muhimman bukatu 5 da ya ke so daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya gabatar da bukatun ne a yayin ganawarsa da wata tawaga daga kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus) kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa Atiku Abubakar ya yi gargadin cewa hankulan mutane yana tashi a halin yanzu a yayin ganawarsa da Abdulsami tare da abokin takararsa Peter Obi da sauran jiga-jigan jam'iyyar PDP.

Ga dai bukatun da ya gabatar kamar yadda aka ruwaito.

1. A bude dukkan asusun ajiyar banki na 'yan jam'iyyar hamayya da aka rufe

2. A dena tura sojoji wuraren zaben da za a gudanar a nan gaba

3. A rika tantance masu zabe kafin a fara kada kuri'u a sauran zabukan da su kayi saura

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

4. INEC ta bude shafinta na Intanet ta yadda dukkan jam'iyyun siyasar da ke takara za su iya shiga su duba yadda abubuwa ke gudana

5. A saki dukkan 'yan siyasar da ake tsare da su ba bisa kan ka'ida ba

Atiku ya kuma ce zaben ranar 23 ga watan Fabrairu itace zabe mafi muni tun bayan da Najeriya ta koma mulkin demokradiya inda ya ce an tafka magudi kuma ba a bawa al'umma abinda suke so ba.

Ya lissafa matsalolin da suka faru a zabe kamar haka

1. Tura sojoji wurin zabe wanda ya sabawa kundin tsarin mulki da umurnin kotun koli

2. Tafka magudi da INEC da jam'iyyar APC da dakarun soji suka hada kai suka yi

3. Kulla makirci tsakanin gwamnatin tarayya da INEC domin kawo cikas ga zabe

4. Kura-kuren da aka tafka a zaben ya nuna cewa ba bu wata cigaba da aka samu bayan zaben 2015

An ruwaito cewa Abdulsalami da tawagarsa sun ziyarci Atiku ne domin tabbatar da cewa babu wata matsala da za ta kuna kai a kasar. Ana sa ran NPC za ta gana da shugaba Buhari domin ta gabatar masa da bukatun Atiku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel