Miji na yana neman Yaran da mu ka haifa – Inji wata Mata

Miji na yana neman Yaran da mu ka haifa – Inji wata Mata

Wata Baiwar Allah mai suna Tope Ogba ta bada labarin yadda Mijin ta mai suna Gabriel Ogba ya ke yi wa ‘Ya ‘yan da su ka haifa fyade. Tope Ogba ta fadawa kotu wannan mugun labari ne a Garin Legas.

Miji na yana neman Yaran da mu ka haifa – Inji wata Mata
Wani mutumi yana aukawa yaran sa har da mai shekara 13
Asali: Depositphotos

Wannan mata take cewa Mijin ta na aure, yana neman Yaran su ‘yan mata masu shekaru 20 da kuma mai shekara 25 a Duniya. Baiwar Allah tace lamarin mai gidan na ta bai tsaya nan ba inda ta kai yana neman karamar kanwar su.

A farkon makon nan Tope Ogba ta sanar da wani kotu mai karbar laifuffuka na musamman da ke cikin Garin Ikeja a jihar Legas yadda Mai gidan na ta yake yi wa yarinyar su ‘yar auta da ba ta wuce shekaru 13 da haihuwa a Duniya ba.

Matar take fadawa hukuma cewa wannan abu ya dade yana faruwa ba tare da sanin ta ba. Sai dai kwanan nan ne karamar yarinyar mai shekara 13 ta tona asirin duk abin da jama’a su ke ta rade-radi a cikin gari ba tare da sanin ta ba.

KU KARANTA: Lauya ya fadawa Atiku cewa ya rungumi kaddara game da zaben 2019

Mahaifiyar wannan yara tace ta fara jin kishin-kishin ne a gari, kuma ko da ta tasa yaran na ta a gaba, sai su ka nuna mata cewa babu shakka Uban su yana kwana da su. Shi dai Mahaifin yayi kokarin musanya wannan zargi da ake masa.

Misis Tope ta fadawa kotu cewa sai dai ta kai Limamin su ya boye ‘yar autar domin gudun Mahaifin na ta ya auka mata. Ita kuma tace tun lokacin Mijin na ta yake yi mata dukan tsiya har yayi kokari ya kona gidan ta bayan yayi mata kaca-kaca.

Yanzu dai an wuce da wannan mutumi zuwa babban gidan kurkukun na kirikiri bayan tsare sa da ‘yan sanda su ka yi a Agege da Morogbo. Ana cigaba da shari’a inda Alkali Sururat Soladoye take bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel