Yaki da cin hanci gadan-gadan, ginin hanyoyi da sauran abubuwan da ake sa ran gani a Najeriya

Yaki da cin hanci gadan-gadan, ginin hanyoyi da sauran abubuwan da ake sa ran gani a Najeriya

A makon nan ne labari ya ratsa Duniya cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari wanda yake kan karagar mulki ya sake lashe zaben shugaban kasa. Tuni dai aka soma aika masa sakon barka ana yi masa fatan alheri daga ko ina.

Yaki da cin hanci gadan-gadan, ginin hanyoyi da sauran abubuwan da ake sa ran gani a Najeriya
Jama'a sun ci burin ganin an samu canji a Gwamnatin Buhari
Asali: Facebook

Mun kawo maku wasu abubuwa da ake tunani za su faru a a Najeriya a wannan karo na biyu da shugaban kasar zai kafa gwamnati. Seyi Ojeleye, wani Masani a kan sha’anin gwamnati ya fadi wasu abubuwa da ake sa rai za su faru.

Daga cikin abubuwan da ake hasashe akwai:

1. Yawaitar kudin shiga

Za a samu karuwar kudin da ke shigowa Najeriya a halin yanzu a dalilin tazarcen shugaba Buhari. Hankalin masu zuba hannun jari zai natsu da cewa akalla za su yi shekaru 4 su na aiki a Najeriya.

2. Inganta wutan lantarki

Ana sa rai cewa gwamnatin Najeriya za ta cigaba da kokarin da ta ke yi wajen cigaba da habaka wutan lantarki. Shugaba Buhari yana yunkurin ganin an inganta karfin wutan da Najeriya ke samu.

KU KARANTA: Mutane na fadin abubuwan da ya dace Buhari yayi a wa’adin sa na karshe

3. Gina hanyoyi da layin dogo

Gwamnatin shugaba Buhari tayi azamar gina hanyoyi na titi da kuma layin dogo na jirgin kasa. A wannan wa’adi na gwamnatin APC, babu mamaki a cigaba da ba wadannan bangarori karfi a kasar.

4. Rikici da ‘Yan Majalisa

A wannan karo, sa-in-sar da ake samu tsakanin masu rike da madafin iko da kuma majalisa zai ragu kwarai da gaske inji masu nazari a harkar siyasa. APC za ta samu rinjaye da cikakken iko kan harkar Majalisu.

5. Yaki da cin hanci da rashawa

Mutane na hangen cewa gwamnatin nan za ta fi bada karfi wajen yaki da rashin gaskiya a wannan wa’adi na biyu. Hukumomin gwamnati irin su EFCC za su samu gudunmuwa daga bangaren majalisa wajen yakar barayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel