2019: Mufti Menk yayi wa Buhari addu’a bayan ya lashe zaben Najeriya

2019: Mufti Menk yayi wa Buhari addu’a bayan ya lashe zaben Najeriya

- Shehin Malami Mufti Menk ya aikawa Buhari sakon murnar lashe zaben 2019

- Babban Malamin addinin yayi wa Shugaban kasar da kuma Najeriya addu’o’i

2019: Mufti Menk yayi wa Buhari addu’a bayan ya lashe zaben Najeriya
Mufti Menk yayi wa Najeriya albarka bayan ya ji sakamakon zabe
Asali: Twitter

Mun samu labari jiya cewa babban malamin nan na addinin Musulunci na Duniya mai suna Mufti Menk yana cikin wadanda su ka taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna na lashe zaben Najeriya da aka yi a makon da ya gabata.

Shahararren malamin na addini wanda asalin sa mutumin kasar Zimbabwe ne ta nan Nahiyar Afrika ya nuna farin cikin sa game da nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shugaban kasar Najeriya inda har yayi masa addu’a.

KU KARANTA: An damke wadanda su kayi wa Buhari ature da duwatsu wajen kamfe

Shehin Malamin yayi wannan jawabi ne a shafin sa sada zumunta da ke kan yanar gizo a Tuwita. Malamin musuluncin yayi wa shugaban kasar fatan alheri da nema masa taimakon Allah wajen gudunar da mulki bayan taya sa murna.

Menk yayi addu’a Ubangiji ya kare shugaban na Najeriya sannan kuma yayi masa jagora a harkar shugabancin kasar da zai cigaba da yi. Malamin ya kuma yi addu’ar cigaba da zaman lafiya a cikin kasar ta Najeriya kamar yadda ya saba.

A zaben da aka yi shugaba Muhammadu Buhari na APC ya tika babban abokin takarar sa watau tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuri’u 15, 191,847 da kuma 11,262,978.

Ga dai yadda yayi jawabin nan cikin Ingilishi:

Congratulations @MBuhari upon your reelection! May the Almighty protect you, continue to bless you & guide you to the best decisions. May peace & prosperity prevail! Aameen #Nigeria #Alhamdulillah pic.twitter.com/b5MlZ33zky

— Mufti Ismail Menk (@muftimenk)

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel