Shugaban kungiyar kwadago ya yi murabus bayan samun mukami a gwamnati
Jibrin Banchir, shugaban kungiyar kwadago (NLC) reshen jihar Filato, ya ajiye mukamin sa bayan gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya bashi mukamin mai bashi shawara a kan harkokin na musamman.
Banchir, shugaban NLC na tsawon shekaru 8, ya sanar da hakan ne yayin taron shugabannin kungiyar kungiyar NLC reshen jihar Filato da aka yi a garin Jos.
Shugaban mai barin gado ya mika ragamar harkokin kungiyar a hannun Yarlings Gumshing, tsohon shugaban kungiyar malaman makaranta, wanda zai cigaba da rikon mukamin zuwa watan Afrilu da za a gudanar da zaben shugabanni.
Ya yi godiya ga ma’aikata bisa damar da su ka bashi na shugabantar kungiyar.
“Duk wani abu da na samu da kuma gogewar da na yi duk dalilin NLC ne. Ba zan taba mantawa da irin gwagwarmaya da fadi tashin da mu ka yi ba a NLC.
“Akwai lokutan da ba za mu iya kwanciya mu yi barci a gidajen mu ba saboda barazana ga rayuwar mu. Akwai lokutan da mu ke kwana a sakatariyar mu don neman hakkin ma’aikata.
DUBA WANNAN: Kar ku tsangwami ‘yan jam’iyyar adawa – Rokon Buhari ga masoya da mgoya bayan sa
“Kazalika haka iyalan mu ke kasa bacci wasu lokutan saboda barazana ga rayuwar su,” a cewar Banchir.
Shugaban mai murabus ya yi godiya ga ubangiji bisa kare shi da ya yi tare da yin addu’ar jin kai ga wadanda su ka rasa ran su sanadiyyar gwagwarmaya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng