Zaben 2019: Atiku ya tika Buhari da kasa a jihar Cross River

Zaben 2019: Atiku ya tika Buhari da kasa a jihar Cross River

A yayin da sauran kiris hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta kammala bayyana sakamakon zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, mun samu cewa Atiku Abubakar ya yiwa Buhari diban Karen Mahaukaciya a jihar Cross River.

A sakamakon babban zaben kasa da hukumar INEC ta gudanar a ranar Asabar ta makon da ya gabata, mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari tumu-tumu a jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya.

Hoton yadda sakamakon zaben jihar Cross River ya kasance daga allon hukumar INEC
Hoton yadda sakamakon zaben jihar Cross River ya kasance daga allon hukumar INEC
Asali: Original

Hoton yadda sakamakon zaben jihar Cross River ya kasance daga allon hukumar INEC
Hoton yadda sakamakon zaben jihar Cross River ya kasance daga allon hukumar INEC
Asali: Original

Atiku yayin yakin zaben sa a jihar Cross River
Atiku yayin yakin zaben sa a jihar Cross River
Asali: Twitter

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, a yayin da Atiku ya samu rinjayen nasara da kimanin kuri'u 295,737, shugaban kasa Buhari ya dauki danga ta rashin sa'a inda ya lashe kuri'u 177,303 kacal a jihar Cross River.

Kazalika wasu Sanatoci uku na jihar karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, sun sake samun nasara ta tazarcen kujerar sa yayin da suka yiwa 'yan takara na jam'iyyar APC mugunyar kaye yayin babban zaben da ya gudana.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Sanatocin sun hadar da; Rose Oko na shiyyar Cross River ta Arewa, Dakta Sandy Onor na shiyyar Cross River ta Tsakiya da kuma Gershom Bassey a shiyyar Cross River ta Kudu. Sandy wanda ya yi nasara a shiyyar jihar ta Tsakiya zai kasance karon sa na farko a zauren majalisar dattawan kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng