Zaben 2019: Atiku ya murkushe Buhari a jihar Delta
Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lallasa shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana sakamakon babban zaben kasa na ranar Asabar.
A yayin da babbar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ke ci gaba da zayyana sakamakon zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, mun samu cewa Atiku ya gasawa Buhari aya a hannu cikin jihar Delta.
Kamar yadda alkalin zabe reshen jihar Delta kuma shugaban jami'ar tarayya da ke garin Otuoke na jihar Bayelsa ya bayar da shaida, Farfesa Seth Accra Jaja ya bayyana cewa, Atiku bai ragawa shugaban kasa Buhari ba yayin da ya yi nasara a kananan hukumomi 23 cikin 25 da jihar Delta ta kunsa.
Farfesa Seth yayin ci gaba da bayar da shaidar yadda ta kaya tsakanin manyan 'yan takarar biyu a birnin Asaba ya bayyana cewa, Atiku ya yi nasa da gamayyar kuri'u 594,068 yayin da Buhari ya tsira da kuri'u 221,292 kacal.
KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno
Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, a yayin da hukumar INEC ke ci gaba da fidda sakamakon babban zabe, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya yiwa shugaban kasa Buhari futu-futu a jihohin Adamawa, Edo, Ebonyi, Bayelsa, Anambra, Enugu, Oyo, Filato, Akwai Ibom, Benuwe, Ondo da kuma Abia.
Tiryan-tiryan ga yadda sakamakon zaben ya kasance cikin kananan hukumomi 25 na jihar Delta tsakanin Buhari da Atiku.
Warri South LGA
PDP 22,086
APC 10,007
Isoko South LGA
PDP 19,407
APC 10,536
Isoko North LGA
PDP 19,515
APC 7,045
Warri South-West
PDP 81,833
APC 43,214
Burutu
PDP 38,543
APC 5,546
Warri North LGA
PDP 25,394
APC 12,744
Sapele LGA
PDP 13,642
APC 9776
Ughelli North
PDP 16,140
APC 24,193
Okpe LGA
PDP 11,167
APC 7,769
Ndokwa West LGA
PDP 20,498
APC 3,579
Bomadi LGA
PDP 62,297
APC 1,742
Ndokwa East LGA
PDP 20,976
APC 3,312
Ethiope East LGA
PDP 8,294
APC 13,854
Ethiope West LGA
PDP 29,458
APC 8,648
Ughelli South LGA
PDP 14,802
APC 10,078
Aniocha North LGA
PDP 12,996
APC 3,674.
Oshimili North LGA
PDP 19,700
APC 1,960
Patani LGA
PDP 17,028
APC 4,789
Ukwuani LGA
PDP 14,681
APC 4,552
Uvwie LGA
PDP 12,712
APC 7,591
Oshimili South LGA
PDP 38,670
APC 2,635
Udu LGA
PDP 10,048
APC 9,166
Aniocha South LGA
PDP 14,770
APC 3,239
Ika South LGA
PDP 20,080
APC 6,378
Ika North-East LGA
PDP 29,331
APC 5,265
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng