2019: PDP ta lashe kujerun Majalisar Tarayya 3 na cikin Abuja

2019: PDP ta lashe kujerun Majalisar Tarayya 3 na cikin Abuja

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi nasarar laske kaf kujerun majalisar tarayya na yankin Abuja. Jam’iyyar adawar ce ta kawo wadanda za su wakilci yankin Abuja a majalisar wakilai da dattawa.

2019: PDP ta lashe kujerun Majalisar Tarayya 3 na cikin Abuja
Aduda na Jam’iyyar PDP ya doke APC a zaben Majalisar dattawa
Asali: UGC

Kamar yadda mu ka samu labari, PDP ce ta ci zaben ‘dan majalisa mai wakiltar yankin na Abuja, inda Philip Tanimu Aduda ya doke ‘dan takarar APC watau Zephaniah Jisalo. Hukumar INEC ta tabbatar da wannan a jiya.

Haka zalika kuma, a kujerun majalisar wakilai na tarayya, Micah Jiba na jam'iyyar PDP ya tika Mustapha Lamorde na jam’iyyar APC. Shi kuma Hassan Sokodabo ya tika ‘dan majalisar Abuja ta kudu wanda ke kan mulki.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya saduda tun kafin a fitar da sakamakon zabe

Micah Jibah zai wakilci mazabar AMAC da Bwari a majalisar tarayya a 2019, Jibah ya samu kuri’a 174, 377 yayin da abokin hamayyar san a APC ya samu kuri’u 82, 761. INEC ta fadi wannan ta bakin Farfesa Rebecca Wusa.

Hukumar INEC ta kuma tabbatar da cewa Hassan Sokodabo ya doke ‘dan majalisar APC na yankin Abuja ta Kudu watau Alhaji Zakari Angulu Dobi. Hassan Sokodabo ya samu kuri’a 81, 023 yayin da APC kuma ta samu 65, 123.

Bayan sanar da sakamakon zaben yankin, Alhaji Hassan Sokodabo yayi godiya a bainar jama'a inda ya kuma yabawa jami’an tsaro game da irin aikin da su kayi ba tare da nuna son kai a babban zaben ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel