Yadda ta kaya tsakanin Atiku da Buhari a jihohi 12 da hukumar INEC ta sanar

Yadda ta kaya tsakanin Atiku da Buhari a jihohi 12 da hukumar INEC ta sanar

Tun bayan kammala kada kuri’u a zaben shugaban kasar Najeriya daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu ne aka fara tattara alkalumman sakamakon zaben daga kowace rumfa, mazaba, karamar hukuma, jaha da ma kasa baki daya, tare da kidayarsu.

Sai dai zuwa yanzu amon mutane biyu kacal ake ji daga cikin yan takarkaru guda saba’in da daya da suka tsayata takarar shugaban kasan, sune yan takarar jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige Dansanda yayin rakiyar sakamakon zabe

Yadda ta kaya tsakanin Atiku da Buhari a jihohi 12 da hukumar INEC ta sanar
Atiku Buhari
Asali: Depositphotos

Kuma duba da sakamakon jihohi guda goma sha biyu da hukumar INEC ta kammala tattarawa, ta kammala kidayarsu kuma ta sanar a babban birnin tarayya Abuja zuwa daren Litinin, sun nuna duka yan takaran biyu suna doke ni, in dokeka, amma fa irin na kuri’u, a jihohi daban daban.

Legit.ng ta ruwaito INEC ta sanar da jihohi goma sha biyu ciki har da Abuja, sauran sun hada da Ekiti, Ogun, Kogi, Kwara, Gombe, Nassarawa, Yobe, Ondo, Abia, Enugu da kuma Ebonyi, yayin da hukumar tace za ta fara da jahar Filato a ranar Talata 26 ga watan Feburairu.

Daga sakamakon da aka sanar, dan takarar jam’iyyar APC Muhammadu Buhari ne ke kan gaba inda ya samu mafi yawancin kuri’u a jihohi guda bakwai da suka kunshi Ekiti, Ogun, Kogi, Kwara, Gombe, Nassarawa, Yobe.

Yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu mafi yawan kuri’u a jihohi guda biyar da suka hada da Ondo, Abia, Enugu, Ebonyi da kuma babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda turawan zabukan jihohin suka tabbatar.

Sai dai a daren jiya ne shugaban hukumar INEC ya sanar da dage cigaba da karbar sakamakon zuwa yau Talata, inda yace za’a cigaba da misalin karfe 10 na safe a babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel