Zaben 2019: Buhari ya yi nasara a jihar Kaduna
Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya lallasa abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.
Fashin baki na sakamakon zaben kamar yadda alkalin hukumar zabe ta kasa reshen jihar Kaduna ya bayyana, Farfesa Bello B. Shehu ya tabbatar da cewa, shugaban kasa Buhari ya samu gamayyar kuri'u 993,445, yayin da Atiku ya lashe kuri'u 649,612 kacal.
Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da shugaba Buhari ya yi nasara a kananan hukumomi 14 cikin 23 da jihar Kaduna ta kunsa, Atiku ya yi nasara a sauran kananan hukumomi 9 bayan kammala kidaya da tantance kuri'u.
Jam'iyyar APC ta yi nasara a kananan hukumomin Kubau, Makarfi, Kudan, Sabon Gari, Ikara, Kauru, Giwa, Soba, Igabi, Birnin Gwari, Zaria, Lere, Kuduna ta Arewa (Kaduna North) da kuma Kaduna ta Kudu (Kaduna South).
Daga bangaren jam'iyyar adawa ta PDP kuma, kananan hukumomi da suka nuna goyan baya ga tsohon mataimakin shugaban kasa sun hadar da; Zangon Kataf, Kaura, Kajuru, Kagarko, Jaba, Chikun, Jema'a, Kachia da kuma Sanga.
Dalla Dalla ga yadda sakamako zaben ya kasance cikin kananan hukumomin jihar Kaduna tsakanin shugaban kasa Buhari da Wazirin Adamawa.
KUBAU LG
APC: 67,140
PDP: 13,296
MAKARFI LG
APC: 36,625
PDP: 14,494
IKARA LG
APC: 44,021
PDP: 14,464
KAURA LG
APC: 6,907
PDP: 33,647
JABA LG
APC: 6,400
PDP: 22,758
KUDAN
APC: 30,577
PDP: 11,697
ZANGO KATAF
APC: 10,411
PDP: 62,622
SABON GARI
APC: 58,467
PDP: 22,644
SOBA
APC: 51,548
PDP: 10,656
KAURU
APC: 33,578
PDP: 27,041
KAGARKO
APC: 16,663
PDP: 21,605
KAJURU
APC: 7,888
PDP: 31,446
GIWA
APC: 45,574
PDP: 9,838
IGABI LG
APC: 97,308
PDP: 20,281
JEMA’A
APC: 19,412
PDP: 61,763
BIRNIN GWARI
APC: 33,786
PDP: 8,206
K/SOUTH
APC: 92,637
PDP: 41,004
ZARIA
APC: 111,082
PDP: 21,882
CHIKUN
APC: 21,930
PDP: 82,909
SANGA
APC: 14,860
PDP: 17,411
KACHIA
APC: 24,905
PDP: 40,337
LERE
APC: 64,299
PDP: 32,426
K/NORTH
APC: 97,514
PDP: 27,185
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng