Zaben 2019: Buhari ya yi nasara a kananan hukumomi 7 cikin 27 na jihar Borno

Zaben 2019: Buhari ya yi nasara a kananan hukumomi 7 cikin 27 na jihar Borno

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya yi nasara a kananan hukumomi bakwai na jihar Borno yayin da sakamakon babban zabe ke ci gaba da kwaranya.

A yayin da sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019 ke ci gaba da bayyana, mun samu cewa, shugaban kasa Buhari ya yi nasara cikin kananan hukumomi bakwai daga cikin 27 na jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a halin yanzu ana ci gaba da tantancewa, kidaya, da kuma fidda sakamakon zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a Kwalejin ilimi ta Kashim Ibrahim da ke birnin Maiduguri.

Zaben 2019: Buhari ya yi nasara a kananan hukumomi 7 cikin 27 na jihar Borno
Zaben 2019: Buhari ya yi nasara a kananan hukumomi 7 cikin 27 na jihar Borno
Asali: UGC

A yayin da manema labarai, jami'an tsaro da dukkanin masu ruwa da tsaki ke tsayuwar daka tare da halartar wannan babban aiki, babban alkalin zabe ne jihar, Saminu Abdulrahman, ya tsaya ka-in da la-in wajen tabbatar da nagarta gami da amincin nauyin da rataya a wuyan sa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Buhari ya yiwa babban abokin adawar sa fintinkau ta fuskar samun yawan kuri'u a kananan hukumomi bakwai cikin 27 da ke jihar Borno kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Hukumar INEC ta bayyana cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha babban kaye a hannun shugaba Buhari cikin kananan hukumomin bakwai da suka hadar da; Nganzai, Mobbar, Dikwa, Abadam, Guzamala, Gubio da kuma Magumeri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel