Ministan Buhari ta lashe kujerar dan majalisar tarayya a Yobe

Ministan Buhari ta lashe kujerar dan majalisar tarayya a Yobe

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da sunan wata minista a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, matar tsohon gwamnan jahar Yobe, kuma matar Sanata, a matsayin wanda ta lashe zaben kujerar majalisar tarayya ta mazabar Damaturu/Tarmuwa.

Legit.ng ta ruwaito wannan ba wata bace illa Hajiya Hadiza Bukar Abba, karamar tsohuwar ministan harkokin kasashen waje a gwamnatin Buhari, kuma uwargidar tsohon gwamnan jahar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi ma yayan jam’iyyar APC kwantan bauna, sun kashe 5

Ministan Buhari ta lashe kujerar dan majalisar tarayya a Yobe
Khadija
Asali: Facebook

Baturen zabe na hukumar INEC, Farfesa Maimuna Waziri ta jami’ar gwamnatin tarayya na Gashua ce ta sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi, 24 ga watan Feburairu a cibiyar tattara alkalumman sakamakon zaben dake garin Damuturu.

Farfesa Waziri ta bayyana cewa Khadija Bukar ta jam’iyyar APC ce ta lashe zaben da kuri’u dubu saba’in da takwas da dari tara da hamsin da uku, 78, 953, iyayin da Alhaji Habu Babayo na jam’iyyar PDP ke binta a baya da kuri’u dubu goma da dari biyar da takwas, 10, 508.

A gaban dukkanin wakilan jam’iyyar PDP da na APC aka sanar da sakamakon zaben, sa’annan dukkaninsu sun rattafa hannu akan sakamakon zaben, wanda hakan ya nuna sun amince da sahihancin sakamakon zaben.

Idan za’a tuna Khadija Bukar ta fafata a zaben fidda gwani ne da babban mijinta, Ibrahim Bukar Abba, inda ta lallasashi a zaben na fidda gwani da kuri’u masu yawa, dama dai daga majalisa Buhari ya daukota ya nadata minista, a yanzu ta koma.

Ita dai Khadija yar gatace a siyasance, duba da cewa Mijinta Bukar Abba ya taba zama gwamnan jahar Yobe na tsawon shekaru goma, kuma a yanzu Sanata ne mai barin gado, mahaifinta Ibrahim Waziri babban dan siyasa ne a jamhuriya ta biyu, kakanta kuma Sir Kashim Ibrahim tsohon gwamnan Arewa a zamanin Sardauna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel