Yan bindiga sun yi ma yayan jam’iyyar APC kwantan bauna, sun kashe 5

Yan bindiga sun yi ma yayan jam’iyyar APC kwantan bauna, sun kashe 5

Wasu gungun yan bindiga sun kashe wakilan zabe na jam’iyyar APC guda biyar a wani harin kwantan bauna da suka kai musu a ranar Lahadi, 24 ga watan Feburairu, kamar yadda rundunar Yansandan jahar Taraba ta tabbatar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kashe wakilan jam’iyyar na APC ne da tsakar daren Lahadi yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida a karamar hukumar Karim Lamido, inda suka gudanar da aikin sa ido a zaben da aka yi.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta musanta batun cafke Buba Galadima

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, David Misal ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace mutanen biyar sun fito ne daga kauyen Umari akan hanyarsu ta zuwa kauyen Cambri, duk a cikin karamar hukumar Karim Lamido a lokacin da aka kai musu harin.

Mista Wisal yace da misalin karfe 3 na dare aka kai ma mutanen harin, amma yace harin bashi da wata alaka da siyasa. “Da gaske ne yan bindiga sun kashe mutane biyar da tsakar daren Lahadi a karamar hukumar Karim Lamido, tuni mun kaddamar da bincike akan lamarin.”

Sai dai kaakakin jam’iyyar APC, Aaron Artmas ya tabbatar da mutuwar guda daya daga cikin wakilan jam’iyyar tasu mai suna Muhammed Kambari, wanda ya gudanar da aikin sa ido akan zabe a kauyensu na Cambri.

“Kambri ya yi mana aikin sa idon zabe a kauyensu ne, amma yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Karim dauke da sakamakon zaben, inda daga nan zai dauki motar da zata kaisu garin Jalingo ne aka bude musu wuta.

“Mun shigar da kara zuwa ga Yansanda, amma har yanzu babu wani sakamako da muka samu, amma muna fatan Yansanda zasu kamo duk masu hannu cikin wannan rikici.” Inji shi.

Shima kaakakin jam’iyyar PDP, Alhaji Inuwa Bakare ya bayyana damuwarsa game da rahoton wannan hari, sai dai ya nesanta jam’iyyarsa da hannu cikin harin, tuni dai an yi ma Muhammed jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel