2019: An kashe mutane wajen rikicin siyasa a Zamfara

2019: An kashe mutane wajen rikicin siyasa a Zamfara

Akalla mutum 3 ne su ka rasa rayukan su a lokacin da rikicin siyasa ya kaure tsakanin Magoya bayan ‘yan siyasa yayin da ake gudanar da zabe a Garin Birnin Magaji da ke cikin jihar Zamfara.

2019: An kashe mutane wajen rikicin siyasa a Zamfara
Mutum 3 sun mutu a Jihar Zamfara saboda rikicin siyasa
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa an yi rigima a Yankin Rumfar Asibiti da ke cikin karamar hukumar Birnin Magaji. Wani wanda abin ya faru a gaban sa yace rikicin ya barke ne lokacin da Magoya bayan wasu ‘yan siyasa su ka hadu.

Wasu ‘Yan APC da ke tare da ‘dan majalisar tarayya na yankin, Aminu Sani Jaji sun gwabza ne da wadanda ke marawa ‘dan takarar PDP watau Alhaji Sani Umar Dangaladima mai neman kujeraar Birnin Magaji da K/Namoda.

KU KARANTA: Ana zargin manyan APC da rudan jama’a da kudi a Zamfara

Wani Bawan Allah mai suna Mal. Jamilu ya bayyanawa ‘yan jarida cewa a kan samu irin wannan hatsaniya a duk lokacin da manyan ‘yan siyasar ke kokarin kada kuri’a musamman a cikin yankin Birnin Magaji da Kauran Namoda.

A sanadiyyar haka ne aka rasa mutane akalla 3 har lahira. Tuni dai aka kira jami’an tsaro inda su ka zo ku kawo tsanaki har abubuwa su ka lafa. Sani Umar Dangaladima yana kokarin karbe kujerar majalisa ne daga hannun Aminu Jani.

Honarabul Aminu Jaji yana cikin wadanda su ka nemi kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar APC mai mulki. Daga baya Aminu Jaji ya janye takarar gwamnan ya koma ya nemi kujerar majalisar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel