2019: Zaben Shugaban kasa ya fara fitowa daga Jihar Katsina

2019: Zaben Shugaban kasa ya fara fitowa daga Jihar Katsina

Ba da dadewa ba mu ka ji labarin cewa APC ta samu kujerar Sanata a yankin Katsina inda Injiniya Kabir Barkiya na APC ya doke ‘dan takarar PDP watau Hamisu Gambo. APC ta samu 340, 8000 inda PDP kuma ta samu kuri’u 124, 372.

Sakamakon zaben da ke shigowa ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne yake samun nasara a jihar sa ta Katsina. APC ce ta ke samun nasara a kananan hukumomi 4 da su ka hada da Ingawa, Daura, Matazu da Kurfi.

2019: Zaben Shugaban kasa ya fara fitowa daga Jihar Katsina
Ana kirga kuri'u a zaben Shugaban kasa da 'yan majalisa Katsina
Asali: Depositphotos

A Garin Ingawa, Buhari na APC ya samu kuri'a 29,230 inda Atiku na PDP ya samu kuri'u. 7,625. Hukumar zabe na INEC ta sanar da cewa a cikin karamar hukumar Kurfi, APC ta samu kuri'a 25,074, yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 9,175.

A Daura kuma inda nan ne Mazabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, INEC ta bayyana cewa APC ta samu 37, 648. Atiku Abubakar ya iya hada kuri'u 4, 650 ne rak. A Garin Matazu kuma APC da PDP sun samu kuri'a 27, 625 da 9, 151 inji INEC

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan Kaduna El-Rufai ya sha kasa a cikin Garin sa

A kujerar Sanata kuma, APC mai mulki ta samu kuri’u 25, 534 yayin da jam'iyyar PDP ta tashi da kuri’a 11, 221. Haka zalika a zaben kujerar majalisar tarayya na Yankin, jam’iyyar APC ta samu kuri’u sama da 25,000 a cikin Garin Matazu.

Sai dai har yanzu ba mu da tabbacin wannan sakamako domin kuwa ba mu ji wani labari daga hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC ba. A inda Buhari yayi zabe dai mun ji cewa APC da PDP sun fadi kujerar Sanatan Katsina ta Arewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel