2019: Atiku da PDP sun yi nasara a akwatin zaben Kwankwaso a Madobi

2019: Atiku da PDP sun yi nasara a akwatin zaben Kwankwaso a Madobi

Mun ji kishin-kishin din cewa jam’iyyar PDP adawa a Najeriya ta yi nasara a zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da aka yi yau a akwati na 003 da ke cikin Garin Madobi a jihar Kano.

2019: Atiku da PDP sun yi nasara a akwatin zaben Kwankwaso a Madobi
Buhari ya ci akwatin El-Rufai ya rasa akwatin Kwankwaso
Asali: Facebook

Wani Hadimin tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana mana cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 156 a zaben shugaban kasa da aka yi a kauyen Sanata Rabiu Kwankwaso. Shugaba Buhari kuma ya samu kuri’a 72.

A can jihar Kaduna da ke kusa da Kano, kuma mun ji cewa gwamna Nasir El-Rufai yayi murna bayan ya ji an sanar da zaben akwatin sa da ke cikin Unguwar Sarki. Shugaba Buhari ya samu kuri’a 369 yayin da Atiku ya samu 44 ne kurum.

KU KARANTA: Sakamakon zaben 2019 daga Yankin Adamawa da kewaye

Jam’iyyar gwamnan mai neman tazarce na APC ce ta lashe sauran zabe na ‘yan majalisar dattawa da majalisar wakilai a Unguwar Sarki da ke cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa inda nan ne gwamnan yake kada kuri’ar sa.

Tsohon gwamna Injiniya Rabiu Kwankwaso ya nemi takarar shugaban kasa a PDP amma ya rasa tikiti a hannun Atiku Abubakar. Wannan ya sa aka nada sa shugaban yakin neman zaben Atiku a PDP a Arewacin Najeriya a zaben na bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel