INEC ta aika kayan aikin zaben jihar Kebbi zuwa Kaduna bisa kuskure

INEC ta aika kayan aikin zaben jihar Kebbi zuwa Kaduna bisa kuskure

- Hukumar Zabe INEC ta yi kuskuren aikewa da kayayakin zabe na jihar Kebbi zuwa jihar Kaduna

- An kuma yi kuskuren aikewa da kayayakin zaben jihar Katsina zuwa Jihar Kebbi

- Kwashinan zabe na jihar Kebbi Ahmad Mahmud ya ce tuni an sanar da INEC kuma ana kan hanyar canjo kayaykin zaben

Kwamishinan Zabe na Jihar Kebbi, Ahmad Mahmud ya ce anyi kuskuren kai wasu daga cikin kayayakin aikin na jihar Kebbi zuwa Jihar kaduna sannan wasu da ya dace a kai jihar Katsina an kai su jihar Katsina.

INEC ta aika kayan aikin zaben jihar Kebbi zuwa Kaduna bisa kuskure

INEC ta aika kayan aikin zaben jihar Kebbi zuwa Kaduna bisa kuskure
Source: Twitter

Mahmud ya yi wannan bayanin ne a yayin da ya ke hira da manema labarai bayan ya gama tantance kayayakin zaben a babban bankin Najeriya da ke jihar Kebbi inda ya ce "Biyu daga cikin fom EC 8D1 da EC 8E1 na jiha Kebbi suna jihar Kaduna yayin da na jihar Katsina kuma an kai su jihar Kebbi.

DUBA WANNAN: Neman shugaban INEC ya yi murabus: MInista ya yi kaca-kaca da Oshiomhole

"Mun gano kuskuren ne a yayin da muke tantance kayayakin zaben kuma a halin yanzu ana hanyar dawo da su jihar Kebbi."

Baturen zaben ya ce INEC reshen jihar Kebbi ta karbi dukkan kayayakin aikin zaben ta na zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya kuma za a fara rabar da su a ranar Laraba a kananan hukumomi 21 na jihar.

Ya ce an gama dai-daita dukkan na'urar card reader na jihar.

"A halin yanzu an gama dai-daita dukkan kayayakin aikin zabe masu muhimmanci na jihar Kebbi da na'urorin card reader kuma a gobe Laraba za mu fara rabar da kayayakin zabe masu muhimmanci"

Ya ce za a gudanar da zabuka a mazabun zabe 2,398 da rumfunan zabe 1,345 da rumfunan zabe 225 da ke jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel