Zan kara koma wa wurin da ‘yan Boko Haram su ka kai min hari – Kashim Shettima

Zan kara koma wa wurin da ‘yan Boko Haram su ka kai min hari – Kashim Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce zai kara bin hanyar zuwa Gamboru daga Maiduguri domin kaddamar da yakin neman zabe a sati mai zuwa duk da kasancewar mayakan kungiyar Boko Haram sun bude wa tawagar sa wuta a kan hanyar a satin da ya gabata.

Mutane uku, cikin su har da wani soja guda, ne su ka rasa ran su bayan mayakan na kungiyar Boko Haram sun kai wa tawagar gwamnan hari.

Sai dai, gwamna Shettima ya bayyana cewar abinda ya faru ba zai taba firgita shi har ya guji zuwa yankin ba. Gwamnan ya kara da cewa ko a wannan karon, zai bi hanyar ne ba tare da ya yi amfani da mota ta musamman da harsashi ba ya yi wa illa ba.

Ya fadi hakan ne yayin ganawa da manema labarai jim kadan bayan kamala wani taron gwamnoni da shugabannin hukumomin tsaro da Buhari ya jagoranta a fadar sa da ke Abuja.

Zan kara koma wa wurin da ‘yan Boko Haram su ka kai min hari – Kashim Shettima
Kashim Shettima
Asali: Facebook

Idan har za a yi la’akari da halin da yankin arewa maso gabas ke ciki a halin yanzu da kuma yadda ya ke a shekaru hudu da su ka wuce, za a fahimci cewar an samu sauki.

“Har yanzu akwai kalubale da barazana amma duk da haka mun yaba wa kokarin shugaban kasa,” a cewar Shettima.

DUBA WANNAN: Zabe: Buba Galadima ya yi wa ubangiji izgili, bidiyo

Sannan ya cigaba da cewa, “ba zai yiwu na ki ziyartar wani bangare a jihar da nake shugabanta ba, ni shugaba ne kuma babban jami’in tsaro a jiha ta. Idan har zan ji tsoron shiga wani yanki a jiha ta, wane sako kenan na aika ga talakawan da na ke shugabanta?

“Mayakan kungiyar Boko Haram na neman wani abu da zai daga sunan su ne, kuma sun samu hakan ta hanyar kai min hari.

Shugabanci na jarumin mutum ne. Zan koma Gamboru Ngala a sati mai zuwa kuma na shirya wa duk abinda zai faru. Ba zan yi amfani da mota mai jure harbin bindiga ba, zan je ne a gama-garin mota kamar yadda ragowar mutanen tawaga ta za su.”

“Ina so ku sani cewar ‘komai nisan dare gari zai waye’, haske zai kori duhu, kuma komai duhun hadari ba za a dawwama ana ruwan sama ba. Wannan haukan na ‘yan Boko Haram zai kare saboda fada ne tsakanin haske da duhu,” a kalaman Kashim Shettima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng