Yaki da ta’addanci: Anyi mutuwar kasko tsakanin Sojojin Najeriya da yan Boko Haram

Yaki da ta’addanci: Anyi mutuwar kasko tsakanin Sojojin Najeriya da yan Boko Haram

Wani kazamin karon battar dakarun Sojin Najeriya da mayakan Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda guda biyar, yayin da Sojoji suka yi asarar jami’ai guda hudu, daga cikinsu har da wani hafsan Soja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mayakan na Boko Haram sun yi kokarin yin dirar mikiya akan dakarun Sojin runduna ta 27 dake jibge a garin Buniya na karamar hukumar Gujba ne, a lokacin da suka yi bata kashin.

KU KARANTA: Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe

Mukaddashin kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fiyar a ranar Lahadi, 17 ga watan Feburairu, inda yace sun kashe yan ta’addan biyar a lokacin da suka yi kokarin tarwasa sansanin Sojojin da misalin karfe 6:5 na yammacin Asabar.

“Duk da yake yan ta’addan sun shirya da gaske don kai harin, duba da yadda suka tunkari sansanin Sojojin cikin motoci masu dauke da bindigu guda hudu, da motar da bata jin bom guda daya da kuma muggan bindigu da alburusai.

“Amma sai da Sojojinmu suka kashe mayakansu guda biyar, sa’annan muka kwace bindigu kiran AK47 guda tara, da wata babbar bindigar baro jirgi guda daya, alburusai da dama, gurneti guda biyu, bamabamai guda hudu, mota mai bindiga daya da babur kirar Bajaj.

“Sai dai mun yi asarar Sojoji guda uku da wani hafsan Soja guda daya, yayin da Sojoji biyar suka jikkata wanda a yanzu haka suna samun kulawa a Asibiti.” Inji mukaddashin kaakaki, Kanal Sagir Musa.

Daga karshe sanarwar ta isar da sakon jinjina da babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya aika ma dakarun Sojin bisa gagarumar nasarar da suka samu akan mayakan Boko Haram, sa’annan yayi kira ga Sojoji da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a kullum don kawo karshen yan ta’adda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel