Zabe: Buba Galadima ya yi wa ubangiji izgili, bidiyo

Zabe: Buba Galadima ya yi wa ubangiji izgili, bidiyo

Jigo a jm’iyyar PDP kuma Tsohon na hannun damar shugaban kasa Buhari a jam’iyyar ANPP da CPC, Buba Galdima, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya cin zaben shugaban kasa ba ko da kuwa ubangiji ne zai kirga kuri’u.

Galadima ya yi wannan kalami ne yayin wata hira da aka yi da shi kuma aka yada ta dandalin sada zumunta na zamani daban-daban.

Da aka tambayi Galadima ko yana ganin, tsakanin sa da Allah, jama’iyyar sa ta PDP na da karfin gwuiwar cin zaben shugaban kasa, sai ya kada baki ya ce, “ai wallahi tallahi billahil lazi la’ilaha illa huwa idan ubangiji ne zai kirga wannan kuri’ar, Buhari sai ya rasa 'deposit'.”

Kalli faifan bidiyon:

Sannan ya cigaba da cewa, “shi da kan sa Buhari ya sani ba zai fadi zabe ba don ba abinda ya tabuka wa kasa, babu abinda ya tabuka wa mutane kuma mun fahimta cewa yanzu zaben ma ba shi za mu zaba ba, Osinbajo za mu zaba, domin shi Buhari da kan say a fadi cewar wasu mutane sun yi ma sa kawanya, sun hana shi tabuka komai.”

Sai dai, bayan faifan bidiyon na Galadima ya fara yawo a dandalin sada zumunta tare da jawo cece-kuce, ya fito ya kare kan sa a cikin wani sabon faifan bidiyon da ya kara fitar wa yau, Lahadi, a shafin sa na Tuwita.

A cikin sabon bidoyon na kare kan sa, Galadima ya yi zargin cewar an canja ma’anar kalaman da ya yi saboda dalilan siyasa.

DUBA WANNAN: ‘Yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC a jihar Benuwe

A cewar sa, “cewa nayi a hira ta da VOA Hausa idan Ubangiji ne zai kirga kuri’u babu yadda Buhari zai iya cin zabe, amma wasu mutane sun je sun sauya abinda na fada saboda tsabar rashin son gaskiya.”

Sai dai jama’a da dama sun kara sukar Galadima a kan kokarin san a kare kan sa tare da bayyana cewar babu banbanci tsakanin kalamin san a farko da na biyu, wanda a cewar su duk izgili ne ga ubangiji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel