Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai farmaki sansanin soji a jihar Yobe

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai farmaki sansanin soji a jihar Yobe

Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya ce a halin yanzu mayakan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki a sansanin sojoji na 27 task force brigade da ke Buni yadi a jihar Yobe kamar yadda mazauna kauyen suka bayyana.

Daily Trust ta gano cewar 'yan ta'addan sun kai farmaki garin ne misalin karfe 5.30 na yamma inda suka iso cikin motocci masu dauke da bindigu.

Wani da abin ya faru a idonsa amma ya nemi a boye sunansa ya ce 'yan ta'adan sun shigo garin ne ta kauyen Amiya da ke kudancin garin sannan suka fado tsakiyar garin.

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai farmaki sansanin soji a jihar Yobe

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai farmaki sansanin soji a jihar Yobe
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

"Ba su taba kowa ba, sun wuce zuwa sansanin sojojin ne sannan suka fara musayar wuta da sojojin. Mu kuma duk mun tsere domin neman mafaka," inji shi.

Ya ce mazauna kauyen sun shige daji domin su tsira da ransu.

A halin yanzu dai ba san ko mutane nawa suka rasu sakamakon harin ba

Ku cigaba da biyo mu domin samun karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel