Siyasa yar ra’ayi: Sarkin Daura ya bayyana ra’ayinsa game da takarar Buhari a zaben 2019

Siyasa yar ra’ayi: Sarkin Daura ya bayyana ra’ayinsa game da takarar Buhari a zaben 2019

Mai martaba sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk ya bayyana goyon bayansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarinsa na zarcewa akan kujerar shugaban kasa, sa’annan yayi kira ga yan Najeriya dasu zabi Buhari a zaben na ranar Asabar.

Sarkin yayi wannan kira ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Feburairu a fadarsa dake garin Daura ta jahar Katsina jim kadan bayan isan Buharin fadarsa, inda yace akwai bukatar yan Najeriya su sake zaben Buhari domin cigaba da kyawawan ayyukan cigaba da yake yi.

KU KARANTA: Siyasa rigar yanci: Labarin wata fitacciyar jarumar Kannywood dake mutuwar son Buhari

“Ina da yakinin Najeriya za ta cigaba da samun cigaba a tattalin arziki, siyasa, tsaro, ababen more rayuwa da kuma noma idan har aka sake zaben shugaban kasa Buhari a karo na biyu, ko a yanzu haka yan Najeriya na alfahari da kasarsu a duk suke a fadin duniya saboda Buhari.

“Ka dawo da martabar Najeriya ta kyakkyawar shugabanci, don haka zamu cigaba da baku goyon baya a tsare tsare da kuma shirye shiryen da gwamnatinka da take yi ma yan Najeriya wadanda zasu kai kasar ga gaci.” Inji Sarkin Farouk.

Da yake nasa jawabin, Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya gode ma yan Najeriya bisa gudunmuwar da suke baiwa gwamnatinsa, sa’annan yayi kira da kada su cire rai dashi a kokarin da yake yi na tabbatar da cika alkawurran da ya daukan musu.

Haka zalika Buhari ya bayyana jin dadinsa da yadda Daurawa suka tarbeshi da kuma kyakkyawar tarbar daya samu a fadar Sarkin Daura, inda suka shirya masa hawan daba, da wannan yace tabbas sun nuna masa shi dansu ne, kuma dansu ya zo gida.

Buhari ya samu rakiyar gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau, ministan sufurin jirgin sama, Hadi Sirika, ministan ruwa Suleiman Adamu da kuma sauran jiga jigan jam’iyyar APC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel