Siyasa rigar yanci: Labarin wata fitacciyar jarumar Kannywood dake mutuwar son Buhari

Siyasa rigar yanci: Labarin wata fitacciyar jarumar Kannywood dake mutuwar son Buhari

Siyasa aka ce rigar yanci, kuma dama shan koko ai daukan rai, haka zalika abinda wani ke so, wani kuma shi yake, hakanan Allah Ya halicci dan Adam, wannan ne dalilin da tasa aka samu rarrabuwar kai a masana’antar Kannywood game da zaben Buhari da Atiku a 2019.

Masana’antar Kannywood ta taka rawar gani matuka a siyasar 2019, domin kuwa duk dan takarar daya samu nasara tsakanin Atiku da Buhari, toh lallai akwai gudunmuwar jaruman fina finan Kannywood a nasarar daya samu.

KU KARANTA: Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka ya kira Buhari ta wayar tarho

Siyasa rigar yanci: Labarin wata fitacciyar jarumar Kannywood dake mutuwar son Buhari

Hadiza da Asase
Source: UGC

Annan Tijjani Asase, wani jarumin Fina finan Kannywood ne ya bada shaida akan wata fitacciya kuma mashahuriyar jarumar Kannywood da tauraronta ke haskakawa, watau Hadiza Gabon, wanda yace tana matukar son shugaba Buhari, har hawaye ta taba zubarwa saboda zaben Buhari.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Maje El-Hajeej Hotoro ne ya bayyana labarin a shafinsa na Facebook, inda yace Tijjani Asase ya tabbatar da soyayyar da Hadiza Gabon keda ita ma Buhari, har yake ganin da wuya a samu kamarta a duk fadin Arewacin Najeriya.

“….Ni na shaida, a arewa nan ta mu, samun mace mai son Baba Bahari kamar Hadiza, aiki ne. Zaben Buhari na farko muna kasar Nijar muna aiki, Hadiza tace Wallahi sai ta dawo Najeriya ta zabi Baba. A lokacin an rufe Boda hankalinta ya tashi harda kuka, wallahi har sai da aka samu ma'aikatan na can da na nan da kyar aka barta, ta shigo kasar nan. kuma baza ka taba ganin ta a wajen yi da Buhari ba…” Inji shi.

Daga karshe Asase ya karkare shaidar Hadiza Gabon da cewa “Kuma har kudinta take kashewa kan a zabi Buhari. Yanzu ma gashi ya kamata ta bar kasar nan dan ci gabanta taki ta tsaya sai ta zabi Baba Allah Ya saka miki dije.'”.

A wani labarin kuma tauraro a masana’antar Kannywood, Adam A Zango ya sauya ra’ayinsa game da takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya janye goyon bayan da yake masa a baya, ya rungumi takarar Atiku Abubakar ganga ganga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel