Ba mu canza yatsar da ake dangwala kuri’a da ita ba – Inji INEC

Ba mu canza yatsar da ake dangwala kuri’a da ita ba – Inji INEC

- INEC tayi karin haske game da yadda za a dangwala kuri’a a zaben bana

- Hukumar zaben na kasa tace ana iya amfani da kowane yatsa wajen zabe

- Ana rade-radin cewa duk wanda yayi zabe da babban yatsa ya rasa kuri’a

Ba mu canza yatsar da ake dangwala kuri’a da ita ba – Inji INEC
INEC tace ko da wani yatsa za a yi dangwala kuri'a
Asali: Depositphotos

Mun samu labari jiya cewa hukumar zabe na kasa watau INEC, ta bayyana cewa maganar da ake ta yadawa na cewa an canza yatsar da ake amfani da shi wajen dangwala kuri’a a zaben da za ayi kwanan nan sam ba gaskiya bane.

Hukumar zabe mai zaman kan-ta na INEC, tace masu kada kuri’a za su iya amfani da kowane yatsa su ka ga dama wajen dangwalawa zabin su. INEC tace babu ruwan takardun ta da yatsar da aka yi amfani da shi wajen kada kuri’a.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019 inji Abdulmumini Jibrin

INEC dai tayi wannan sanarwa ne a shafin na sadarwa na zamani na Tuwita jiya Ranar Laraba domin kauda shakkun da aka jefawa jama’a na cewa duk wanda yayi amfani da babban yatsa wajen zabe, yayi asarar kuri’ar sa a banza kurum.

Kamar yadda mu ka ji, hukumar zaben ta ja hankalin jama’a cewa su yi kokarin ganin su dangwalawa jam’iyyar da su ke so a wajen rukunin da aka kebe. Muddin tawadar da aka sa ya haura zuwa layin wata jam’iyya, an yi asara.

A Ranar Asabar dinnan ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisar tarayya a fadin Najeriya. Hukumar na zabe mai zaman kan-ta, tace ba ta da niyyar kawo sabon tsari na yadda za a kada kuri’a a wannan zabe da za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel