Idanun duk Duniya na kan zaben Najeriya na bana – Inji Janar Babangida

Idanun duk Duniya na kan zaben Najeriya na bana – Inji Janar Babangida

Yayin da babban zaben Najeriya ya gabato, mun samu labari cewa tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida yayi magana game da wannan zabe inda ya ba daukacin al’ummar kasar shawara.

Idanun duk Duniya na kan zaben Najeriya na bana – Inji Janar Babangida

Janar Babangida ya nemi ayi zaben Najeriya lafiya babu rikici
Source: Depositphotos

Tsohon shugaban kasar yayi magana ne da ‘yan jaridar nan ta DW yana mai roko ayi zaben na Najeriya cikin lumuna da zaman lafiya ba tare da an kawo wani tashin hankali da zai kai ga asarar rayuka da dukiyar mutane.

Janar Badamasi Babangida ya kuma ja hankalin jama’a da cewa su san cewa Duniya ta zura idanu tana kallon yadda zaben kasar zai kasance, don haka ya nemi jama’a su tabbatar an yi zaben cikin lumuna ba tare da hatsaniya ba.

KU KARANTA: Kasar waje su na ba Atiku fifiko a zaben Najeriya – Inji Buhari

Haka zalika tsohon shugaban na Najeriya ya aika nasihar sa ga Matasa yana mai gargadin su cewa su guji bari ana amfani da su wajen tada fitina a lokacin zabe. Ibrahim Babangida ya kuma yi nasiha ga masu neman kujeru.

Babangida yana cewa bayan zabe bai kamata nasara ko faduwa zabe ta haddasa gaba a tsakanin juna ba inda kuma yace ya kamata Matasan su san cewa wata rana su za su rike Najeriya don haka su zama masu kawo lumana.

Ibrahim Babangida mai shekaru 77 a Duniya yayi wannan jawabi ne ta wani bidiyo da ya shigo hannun mu. Janar Ibrahim Babangida ya mulki Najeriya na tsawon shekaru tun daga 1985 har zuwa 1993.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel