Zabe: Ingila tayi barazanar daukan tsauraran matakai a kan 'yan siyasar Najeriya

Zabe: Ingila tayi barazanar daukan tsauraran matakai a kan 'yan siyasar Najeriya

- Kasar Ingila tayi barazanar kwace kadarorin 'yan siyasa da suke yada kalaman kiyaya ko kuma biyan 'yan daba su kawo cikas ga zabe

- Ingilan da kuma ce za ta haramtawa irin wadannan yan siyasar shiga kasar ta tare da gurfanar da su a gaban kuliya

- Jakar Ingila a Najeriya, Catriona Liang ta ce za tayi aiki tare da kungiyoyin sa kai domin sanya ido a kan yadda zaben zai gudana

Babban jakadar Kasar Ingila a Najeriya, Catriona Laing ta gargadi 'yan siyasar kasar da cewa za a haramta musu shiga Ingila tare da kwace kadarorinsu da ke kasar muddin aka same su da hannu cikin tayar da fitina yayin zaben ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu.

Ms Laing ta bayar da wannan gargadin ne a yayin wani taron manema labarai da ta kira a ranar Laraba a Abuja domin kaddamar da dakin sanya ido a kan yadda zabe ke tafiya da kungiyoyin sa kai suka bude a Abuja.

DUBA WANNAN: Mutuwar magoya bayan jam'iyyar APC: Buhari ya mika sakon ta'aziyya

Zaben 2019: Ingila tayi barazanar daukan mataki a kan 'yan siyasan Najeriya

Zaben 2019: Ingila tayi barazanar daukan mataki a kan 'yan siyasan Najeriya
Source: UGC

Ta ce tunatar da 'yan siyasar cewa baya ga kwace kadarorinsu da za a yi, akwai yiwuwar gurfanar da su a gaban kuliya idan aka same su da hannu cikin tayar da fitina.

"Ba zamu nuna fifiko ga wata jam'iyya ba saboda haka za mu sanya ido a kan dukkan 'yan siyasa masu yadda kalaman kiyayya.

"Mun damu matuka a kan kalaman kiyaya da aka furta a wurin yakin neman zaben jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma muna gargadi a kan irin wannan kalaman.

"Damuwar mu ba ta tsaya bane kawai ga yadda 'yan sanda za su samar da tsaro yayin gudanar da zabe, muna duba da irin rawar da al'umma ke takawa wurin tayar da husuma da kalamansu ko kuma biyan 'yan daba su kawo cikas ga zabe.

"Wata matsalar kuma itace yada labaran karya shi yasa za muyi aiki tare da kungiyoyin sa kai domin samun ingantattun bayanai," inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel