Kungiyar Tijjaniya tayi karin haske a kan goyon bayan takarar Buhari
- Jigo a darikar Tijaniyah, Sheikh Ibrahim Maqari ya ce Tijaniyah ba ta tsayar da wani dan takara da mabiyanta za su zaba ba
- Ya ce dukkan mabiya darikar Tijaniyah suna da ikon zu zabi duk wanda ransu ya natsu da shi sai dai an shawarcesu su zabi mutanen kirki masu gaskiya da kishin kasa
- Sheikh Maqari ya nesanta darikar Tijaniya da wata kungiya mai suna Tijjaniya SUFI Movement of Nigeria da ta fito da ce mabiyanta su zabi Shugaba Buhari
Jigo a darikar Tijaniyyah na Najeriya, Sheikh Ibrahim Maqari ya nesanta kungiyar daga goyon bayan tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zabe na ranar 6 ga watan Fabrairu.
A dai ranar Lahadi ne wata kungiya mai suna “Tijjaniya SUFI Movement of Nigeria” ta yi kira ga magoya bayanta a dukkan sassan Najeriya su zabi Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.
DUBA WANNAN: Zabe: RTEAN tayi alkawarin bawa Buhari kuri'u miliyan 16
A sanarwar da kungiyar ta fitar da hannun shugabanta, Timasaniyu Ahmed-Rufai, kungiyar ta ce ta cimma matsayar goyon bayan Buhari ne karo na biyu saboda "an gwada shi kuma an gamsu da nagartarsa".
Sai dai Sheikh Maqari wanda shine babban limamin a Masallaci na Abuja ya nesanta kungiyar ta Tijaniyya daga wannan goyon bayan inda ya ce dukkan 'yan kungiyar su zabi duk wanda suke so bisa abinda zuciyarsu ta gamsu da shi.
"Tijanniyah tsari ne na sufanci ba kungiya ba. Tijaniyah ba ta tilastawa mabiyanta zaban wani dan takara ba," inji Maqari.
"Abinda shugabanin Tijyaniyah suka ce shine mabiyansu su zabi shugabani masu gaskiya da rikon amana, halaye na gari da kishin kasa ba tare da la'akari da jam'iyyun siyasar da suke ciki ba.
"Kowa zai kare zabin da ya yi a gaban Allah (SWT) a gobe kiyama."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng