Zabe: RTEAN tayi alkawarin bawa Buhari kuri'u miliyan 16

Zabe: RTEAN tayi alkawarin bawa Buhari kuri'u miliyan 16

- Kungiyar masu daukan ma'aikatan sufuri da direbobi na kasa RTEAN ta ce Shugaba Muhammadu Buhari za ta mara wa baya a zaben 2019

- RTEAN ya cimma wannan matsayar ne duba da ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa da gwamnatin Buhari ke samarwa

- Kungiyar ta kuma yiwa shugaba Buhari alkawarin kuri'u fiye da miliyan 16 saboda tana da mambobin da suka dara wannan adadin a fadin Najeriya

Zabe: RTEAN tayi alkawarin bawa Buhari kuri'u miliyan 16
Zabe: RTEAN tayi alkawarin bawa Buhari kuri'u miliyan 16
Asali: UGC

Kungiyar Masu Daukar Ma'aikatan Sufuri da Direbobi ta Najeriya (RTEAN) ta sanar da goyon bayan ta ga takarar Shugaba Muhammadu Buhari a babban zaben ranar 16 ga watan Fabrairu tare da yin alkawarin bawa shugaba Buhari kuri'u miliyan 16 a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar na kasa Osakpamwan Eriyo a yayin wata hira da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.

DUBA WANNAN: Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa

A cewarsa, kungiyar tana da mambobi sama da miliyan 16 wadda suka hada kai wuri guda domin zaban dan takara guda daya da kungiyar ta amince da shi.

"Muna goyon bayan Buhari ne saboda ya yiwa Najeriya ayyuka sosai tun hawansa kan mulki, za ku iya ganin yadda muke da tituna masu kyau a yanzu.

"Muna da hannun jari a kasar nan kuma idan babu zaman lafiya, sana'ar mu ba za ta yiwu ba. Muna da mambobi fiye da miliyan 16 a Najeriya, hakan yasa muke kira garesu su zabi Buhari saboda ya cigaba da ayyukan alheri da ya fara.

"Saboda idan muka sake zabensa, dukkan ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa da gwamnatinsa ke samarwa za su cigaba, hakan yasa muke goyon bayan shugaban kasa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel