2019: El-Rufai ya bayyana manyan dalilai guda 4 kwarara da zasu kayar da Atiku

2019: El-Rufai ya bayyana manyan dalilai guda 4 kwarara da zasu kayar da Atiku

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, wanda yayi kaurin suna wajen nuna adawa ga dan takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake bara, inda yayi kira ga yan Najeriya da kada su zabi Atiku a zaben 2019.

Ga masu bibiyan siyasar Najeriya sun sani sarai cewa Atiku da El-Rufai sun dade basa ga maciji tun a zamanin mulkin Obasanjo, lokacin da Atikun ke mataimakin shugaban kasa, El-Rufai kuma yake rike da mukamin shugaban hukumar sayar da kadarorin gwamnati.

KU KARANTA: Miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Mata guda 2 a Kaduna

2019: El-Rufai ya bayyana manyan dalilai guda 4 kwarara da zasu kayar da Atiku

2019: El-Rufai da Atiku
Source: UGC

El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Premium Times, inda ya bayyana wasu manyan dalilai guda hudu dayake ganin sun isa su hana yan Najeriya zaben Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Feburairu.

A cewar El-Rufai: “Bai kamata yan Najeriya su zabi Atiku ba saboda bashi da wani tarihin tsantsani da rike amana a aikin gwamnati, bai kamata a zabi Atiku ba saboda bashi cikakken sanin hakkokin da suka rataya a wuyan ma’aikacin gwamnati.

“Bai kamata yan Najeriya su zabi Atiku a matsayin shugaban kasa ba saboda baya iya bambamce bukatar kashin kai da bukatar jama’a, a wajensa bukatar kashin kai da ta jama’a duk daya ne. haka zalika bai kamata su zabeshi ba saboda baya damuwa da mutunci da kimar jama’a.” Inji shi.

El-rufai ya bayyana cewa duka wadannan abubuwa daya zayyana ya fuskancesu a tarayyarsa da Atiku Abubakar, don haka shi ganau ne ba jiyau ba, shi yasa ba zai taba zabensa ba, kuma yake kira ga yan Najeriya da kada su zabeshi.

Bugu da kari El-Rufai ya tuna ma yan Najeriya cewa alkawarin da Atiku yayi na azurta abokansa gaskiya ne, don haka duk wanda ya yanke hukuncin zabensa a matsayin shugaban kasa ya tabbata yana cikin rukunin abokansa, idan ba haka ba kuwa ya lashe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel