'Yan takarar Kujerar shugaban kasa 15 masu shaidar kammala karatun Sakandire

'Yan takarar Kujerar shugaban kasa 15 masu shaidar kammala karatun Sakandire

Yayin da ya rage sauran kwanaki biyar kacal a gudanar da babban zaben kasa na kujerar shugaban kasa a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, akwai jerin 'yan takara 72 masu hankoron kujerar mulki da kuma akala ta jagorancin kasar nan.

Sakamakon fitar da jerin sunayen 'yan takarar dukkanin wata kujerar siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta wassafa, akwai jerin 'yan takarar kujerar shugaban kasa da kuma abokanan takarar su 144 da za su fafata a zaben bana.

'Yan takarar Kujerar shugaban kasa 15 masu shaidar kammala karatun Sakandire

'Yan takarar Kujerar shugaban kasa 15 masu shaidar kammala karatun Sakandire
Source: Twitter

Cikin dukkanin 'yan takarar, akwai kimanin ashirin da suka gabatar da shaidar su ta kammala karatun sakandire a matsayin mafi koluluwar matakin ilimi da suka taka a rayuwar su kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mafi shahara cikin sun hadar da shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da wasu 'yan takarar 14 na daban da tuni suka mika takardun su na shaidar karatu ga hukumar INEC yayin tantance su.

KARANTA KUMA: 2019: Jerin wadanda ba za su yi zabe ba a bana

A yayin da wasu ke bayyana ra'ayin sauya wannan doka ta amfani da takardar shaidar kammala karatun sakandire a matsayin cancantar takarar kujerar shugaban kasa, wasu ko sun bayyana amincewar su akan wannan shimfidar tsari da kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi.

Ga jerin sunayen 'yan takara 15 tare da jam'iyyun su da suka gabatar da shaidar su ta kammala karatun sakandire a matsayin mafi kololuwar matakin ilimi da suka taka a rayuwar su:

1. Muhammadu Buhari - APC

2. Omoyele Sowore - AAC

3. Shipping Moses Godia - ABP

4. Umenwa Godwin - AGAP

5. Okere Evelyn - ANR

6. Gbor John Wilson - APGA

7. Obinna Ochechukwu - APP

8. Abah Lewis Elaigu - CAP

9. Muhammad Ali - DPP

10. Sunday Eguzolugo - JMPP

11. Azael Vashim - Liberation Movement

12. Hamza Al-mustapha - PPN

13. Isa Bashayi - MMN

14. Ahmed Buhari - SNP

15. Nnadu Nnamdi Edozie - Independent Democrats

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel