Dandalin Kannywood; Sanata Kwankwaso ya damka ma Adam Zango darikar Kwankwasiyya
Zuwa yanzu dai labari ya riga y agama yaduwa cewa mashahurin dan wasan fina finan Hausa da akafi saninsu da suna Kannywood, Adam Zango ya sauya gidan siyasarsa, bayan yayi jifa da gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rungumi takarar siyasar Atiku Abubakar.
Da wannan ne Zangon ya garzaya da kansa ba sako ba zuwa jahar Kano, har gidan jagoran kwankwasiyya, kuma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ya karbi darikar Kwankwasiyya, kamar yadda al’adar siyasar take.
KU KARANTA: Lamidon Adamawa, da wasu manyan Sarakunan Najeriya 2 dake tare da Buhari a zaben 2019
Haka kuwa aka yi, inda isarsa keda wuya, sai suka yi arba da Sanata Rabiu Kwankwaso, nan take ya rusuna a gaban Kwankwaso, shi kuma ya dauki jar hula irinta Kwankwasiyya, ya sanya masa a kai, ta shigeshi tsaf!
Wannan mikawa tare da karbar darikar Kwankwasiyya data faru tsakanin A Zango da Kwankwaso ta wakana ne jim kadan kafin fara gangamin yakin neman zaben Atiku Abubakar daya gudana a filin wasanni na tunawa da Sani Abacha, wanda ya samu halartar dubun dubatan magoya baya.
Idan za’a tuna Legit.ng ta ruwaito wannan mataki da Adam Zango ya dauka na komawa gidan Atiku yayi matukar baiwa jama’a mamaki, musamman wadanda suka san shi a matsayin dan gane kashenin shugaba Buhari a baya.
Sai dai dama a yan kwanakin nan a jiyo shi yana korafin yadda gwamnatin APC ke yi ma yan fim rikon sakainar kashi. Ko a ranar Laraba sai da aka hangi Zango yana watsa kamfe da abokinsa, kuma sanannen mai goyon bayan takarar Atiku Abubakar, Zaharaddeen Sani ya buga a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Instagram, wanda hakan ke nuna ana tare.
Sai dai shima wani shahararren mawakin Kannywood, Naziru Ahmad ya mayar ma A Zango da martani, inda yayi zargin ya koma gidan Atiku ne saboda kudi, don haka yayi kira ga jaruman Kannywood dasu guji wasa da hankulan masoyansu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng