Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Mahaifin Rabilu Musa Dan Ibro ya rasu

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Mahaifin Rabilu Musa Dan Ibro ya rasu

Dukkan mai rai mamaci ne, kuma wani bai rayuwa domin wani, gaskiyar wannan magana ta tabbata inda mahaifin marigayi Rabilu Dan Ibro, fitacce kuma shahararren dan wasan Kannywood, Malam Musa ya rigamu gidan gaskiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malam Musa ya rasu ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Feburairu da misalin karfe 2:30 na rana, kuma a ranar Litinin, 11 ga watan Feburairu za’a gudanar da sallar Jana’izarsa.

KU KARANTA: Lamidon Adamawa, da wasu manyan Sarakunan Najeriya 2 dake tare da Buhari a zaben 2019

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Mahaifin Rabilu Musa Dan Ibro ya rasu

Ibro da mahaifinsa
Source: UGC

Idan za’a tuna a dansa, Dan Ibro ya rasu ne a ranar 9 ga watan Disambar shekarar 2014, yana dan shekara 44 a rayuwa, inda ya rasu bayan fama da rashin lafiyar koda, wannan mutuwa ta dimauta mahaifinnasa kamar yadda ya bayyana.

Cikin wata hira da Malam Musa yayi da wata jarida, ya bayyana cewa rayuwarsa da ta iyalansa gaba daya ba zata taba zama daidai ba sakamakon rasuwar Dan Ibro, saboda shine ke basu duk kulawar da suke bukata. Sai dai kash, ashe shima tasa tana nan tafe bayan kimanin shekaru uku!

Ko a kwanakin baya sai da gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tallafa ma iyalan Dan Ibro a lokacin da suka aurar da diyar Dan Ibro, inda gwamnatin ta hada mata kayan daki gaba daya.

A yanzu haka rahotanni sun bayyana cewa mahaifin marigayi Dan Ibro, Malam Musa, ya rasu ya bar mata, yaya da dama da jikoki da dama, da fatan Allah Ya jikanshi, Ya gafarta masa, Ya kuma albarkanci abinda ya bari a baya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel